A ranar Alhamis ce Wazirin Katsina, Alhaji Sani Abubakar Lugga, ya ajiye rawaninsa bayan takaddamar da ta biyo bayan furucin da ya yi kan halin tsaro da kasar take ciki.
Aminiya ta kuma tabbatar da hakan daga bakin mai magana da yawun masaurautar Katsina, Mallam Iro Bindawa, wanda daga haka bai yi wani karin bayani a kai ba.
- Zanga-zangar kin jinin yaki ta barke a Rasha
- Ukraine ta nemi kasashen duniya su dauki mataki kan mamayar Rasha
Bayanai sun ce hakan na zuwa ne a sakamakon takaddamar da ta biyo bayan wani jawabi da Wazirin ya gabatar a Ilorin, babban Jihar Kwara a kan matsalar tsaro da kasar nan ke ciki baki daya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa a wani taron manema labarai da ya gudana a birnin na Ilorin inda aka yi masa tambayoyi a kan yanayin tsaro da Jihar Katsina ke ciki ne Alhaji Lugga ya ba da bayanin kusan duk abin da manyan Katsina kan furta.
Wannan jawabin nasa, wanda wasu jaridun kasar nan suka dauka a ranar Litinin da ta gabata, ya harzuka masarautar Katsina, lamarin da ya sanya ta rubuta masa takardar tuhuma don neman ya ba da bayani a kan dalilin furucin da ya yi.
A bayanin nasa da ya rubuta, Alhaji Sani Lugga ya ba da hujjojinsa na cewa akwai matsalar tsaro a Katsina har ta shafi Kananan Hukumomi takwas da hujjarsa ta cewa an rufe makarantu kuma wasu Hakimai har sun yi kaura daga masarautunsu.
A ranar Alhamis Wazirin na Katsina ya ba da amsa cikakkiya mai shafuka hudu da kwararran hujjoji har da maganganun Gwamnan Katsina, Sarkin Katsina da Sakataren Gwamnatin Jihar.
Kazalika, Alhaji Lugga ya aika wa Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman takardarsa ta ajiye sarautarsa.
A wasikar da ya rubuta mai shafuka biyu, ya kawo tarihin sarautar gidansu ta Kanem Bakashe da ke kasar Nijar, wadda ta samo asali tun 1579.
Kazalika ya kawo tarihin sarautar Waziri a gidansu, wadda ta fara tun 1906. Ya kuma ba da bayanin yadda aka nada shi Wazirin Katsina a 2002, wanda ya ce a yau Alhamis, 24 ga watan Fabrairun 2022 ya ajiye.
Haka kuma ya yi godiya ga Mai Martaba Sarkin Katsina tare da neman gafararsa idan har hukuncin da ya dauka ya sosa masa rai.
Da Aminiya ta sake bin diddigin lamarin, ta gano cewa a jawabin da Wazirin Katsina na biyar da ya fito daga gidan Sarautar Sullubawa a birnin na Ilorin, ya ce Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari har zuwa ga Mai martaba Sarkin na Katsina babu wanda bai yi magana a kan batun matsalar tsaro ba da kuma yin kira ga jama’a da su tashi su kare kan su.
Sai dai maimaita wannan jawabi ne ya janyo tuhumar da masarautar ta yi ma shi a kan cewa, wa ya sanya shi fadin halin tsaron da jihar take ciki musamman a wani wuri daban.
Da kuma wakilinmu ya kara bincike a kan wannan takaddamar da ta kai shi ga ajiye masarautar rawaninta da kuma bayanan da muka samu daga majiyoyi na kusa da duka sassan biyun, sun nuna cewa, an dade ana zaman doya da manja a tsakanin Sarkin da kuma Wazirin.
Majiyar wadda ta bukaci a sakaya sunanta ta ce, “da abin ya yi kamari sosai, har sai da masarautar ta ja kunnuwan wasu hakimanta da ta san suna da wata alaka ko mu’amulla da shi Wazirin.
Masarautar ta yi kashedin cewa, duk wanda ya sake zuwa inda Wazirin yake ko ya ci gaba da mu’amala da shi, to zai yi hakan ne a bakin rawaninsa.
Kazalika, Aminiya ya gano cewa tun wancan lokacin kafin zuwan wannan hukunci da ya yanke, Wazirin ya rika neman shawarar wasu manya da kuma wasu daga cikin aminansa a kan matakin da ya kamata ya dauka domin tsira da mutunci shi, inda dukkan su suka bashi shawarar ya ajiye wannan mukamin.
“A yanzu dai faduwa ce ta zo daidai da zama, kuma hakan da ya yi ya kare martaba da mutuncin shi da kuma ita masarautar”, kamar yadda majiyar ta bayyana.
Har ya zuwa lokacin da Aminiya ta tattara wannan rahoto, babu wani bayani da ya fito a hukumance daga masarautar a kan wannan lamari, inda hankalin jama’a duk ya karkata domin jin abin da zai biyo baya a kai.