Gwamnatin China ta sanar da cewa ta yi nisa wurin kera makamin nukiliya domin tsare martabarta a idon duniya.
Ministan Tsaron Kasar, Wei Fenghe ne ya sanar da haka a ranar Lahadi a yayin taron koli kan harkokin tsaron yankin Asiya da ke gudana a Singapore.
- ’Yan bindiga sun yi awon gaba da limaman coci 3 a Kogi
- Miloniyan da ya ci gaba da rubuta jarrabawar shiga jami’a bayan ya fadi sau 25
Ministan ya ce shekaru sama da 50 suka kwashe suna kokarin kera makamin.
Tun a shekarar da ta gabata Amurka ta ce ta bankado yadda China ke bunkasa makamashin nukiliya ba tare da sanin duniya ba.
To sai dai ministan tsaron Chinan ya ce burin kasarsa shi ne kokari na dakatar da amfani da makamin kare dangi a duniya ta hanyar kare martabarta.
Mahukunta a Chinan sun ce za su yi amfani da makamin nukiliyar ne kawai a wurin kare kansu, kuma ba za su taba fara amfani da makamin ba, sai idan wani ya fara kawo musu hari da shi.