✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da muka zabi sulhu da ’yan bindiga — Shugaban Yankin Isa

Shugaban Karamar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato Kwamared Abubakar Yusuf Dan Ali a zantawarsa da wakilinmu ya yi magana kan harkar tsaro da siyasa da…

Shugaban Karamar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato Kwamared Abubakar Yusuf Dan Ali a zantawarsa da wakilinmu ya yi magana kan harkar tsaro da siyasa da kuma zaben 2023 da ke tafe da sauransu:

Isa tana cikin kananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro a Gabashin Sakkwato, wace hanya ka bi don ganin cewa harkar tsaro ta inganta fiye da in da aka fito?

Su wadannan mutane (’yan bindiga) duk inda suka cika fitina inda suke ganin ana matsa masu ne.

In sun yi karfi kamata ya yi ka samu hanyar sulhu da su kawai don zaman lafiyar mutanenka da saukin mu’amala.

Mun fi ba da karfi ga sulhu don a tafi gona rani da damina a samu abinci, ba mu da karfin da muke fuskantarsu, soja da ’yan sanda na Gwamnatin Tarayya ce, ba mu ba su albashi da umarni, sai dai mutuntawa a tsakaninmu.

Muna iyakar kokarinmu ta hannun Gwamna, muna zama da kowane bangare muna sanar da su amfanin zaman lafiya da kuncin rashin zaman lafiya, hakan muke yi a koyaushe.

Duk matsalar da ake ciki an ce ka yi wasu abubuwa da mutane ke sambarka, yaya hakan ta samu?

To, ka san kowa da nasa tsarin. Rayuwata abin da ta sa a gaba, ba na son mutum ya zo min da lalura ban yi wani abu a kai ba, bana jin dadin haka.

Ina son in taimaka wa duk wani da ya zo da matsala iya gwargwadon hali. Na fi farin ciki in yi wa mutum abin alheri.

Ina farin cikin ganin jama’ata suna cikin walwala.

Karamar Hukumar Isa ta hada tsohon Gwamna, Alhaji Attahiru Bafarawa da tsohon Ministan Sufuri, Alhaji Yusuf Suleiman da Kwamishinan Harkokin Addini, Alhaji Suleiman Usman Danmadami, kana ganin wata jam’iyya na iya samun nasara a kan PDP a yankin?

A Karamar Hukumar Isa da ka yi maganar Attahiru Bafarawa da Yusuf Suleiman da Danmadamin Isa duk suna cikin jam’iyya daya.

A kawo wata jam’iyya da tunanin za ta yi tasiri za mu ce hira ce.

Abin da ya sa na ce haka, a 2019 abubuwan da aka yi ba boye suke ba, Isa ta taka rawar ganin da ta gwada wa Gwamna Tambuwal kara kuma can ne mahaifar tsohon Gwamna.

A lokacin Alhaji Yusuf Suleiman ba ya cikin PDP, balle yanzu ya dawo ciki da jama’arsa.

Wadannan mutanen ba ababen yarwa ba ne domin suna da jama’a da kyautata masu kuma in sun ce su yi za su yi, in lokaci ya yi za a gani.

Wasu wurare za a ga shugaban karamar hukuma ya yi Gabas sarakunansa sun yi Yamma, yaya ku tafiyarku ta zama daya?

Abin da ke faruwa a misali, in ka duba shi hali zanen dutse ne, na tashi a gidanmu na samu mahaifina yana tare da Sarkin Gobir, Ahmadun Ahmadu Dan Amadu Bawa, ya zauna da Shehu Malami Dan Ahmadu ya kuma zauna da Sarkin Gobir na yanzu.

Sannan Sarkin Gobir Ahmadu yaya ne ga mahaifiyata ko da na tashi na samu gidan sarki gidanmu ne ina neman shawararsu.

Ko da wannan mulki ya zo gare ni ba wanda nake zama da shi sama da Sarki.

Sarkin Gobir na Isa da Bafarawa zaune muke lafiya tare, ina yi musu biyayya suna kauna ta ina kaunar su, muna tafiya abu daya domin ci gaban Karamar Hukumar Isa ba tare da wata matsala ba.

Me za ka ce kan yadda Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya rike shugabannin kananan hukumominsa?

Ka san duk wanda aka haife shi a gidansu yana son mahaifansa a kullum su yi masa addu’ar gamawa lafiya, ya san sun gamsu da abin da suke yi.

Mu ba mu kin yi wa Gwamna Tambuwal adalci domin ko muna nan ko ba mu nan yana tinkaho da cewa ya ji dadi da Allah Ya ba shi mu a matsayin shugabannin kanannan hukumomi na yanzu.

In da da ba mu ne aka samu ba, a halin da ake ciki yanzu da matsalar da za ta zo Sakkwato ba karama ba ce.

Don haka mu mun dauke shi a matsayin uba kamar yadda ya dauke mu ’ya’ya, yana yaba mana, muna yaba masa.

Mun gode da abubuwan da suke gudana a tsakaninmu da shi, yana kokarin kara kyautatawa gare mu don magoya bayanmu su kara sakewa.

Kana ganin yadda Gwamna Tambuwal ya jagorance ku za ku taimaka wa wanda yake so ya gaje shi ya samu nasara a 2023?

Mu a matsayinmu na shugabannin kananan hukumomi cikin 23 na Jihar Sakkwato masu biyayya ga Gwamna Tambuwal muna fada za mu yi tsaye mu tabbatar an samu nasara a zaben 2023.

Za mu yi addu’a mu san karfinmu da basirarmu da jama’armu mu tabbatar mun samu nasarar Tambuwal da mu ba mu ji kunya ba ga tafiyar da za yi ta 2023 da ikon Allah, wanda Tambuwal ya kawo su ne za su gaje shi a wannan jiha.