Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU), ta sanar da tsawaita yajin aikin mako hudun da ta fara yi saboda Gwamnatin Tarayya ta gaza cika alkawuran da suka kulla a shekarar 2020.
Shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Litinin.
- ‘Akwai yiwuwar ASUU ta zarce da yajin aikinta har sai abin da hali ya yi’
- Messi a PSG: Shin kwalliya ta biya kudin sabulu?
A cewarsa, Majalisar Zartarwar Kungiyar ta Kasa a yayin taronta na ranar Lahadi, ya ce sun yanke shawarar tsawaita yajin aikin da mako takwas don ba gwamnatin damar aiwatar da yarjejeniyar.
Sanarwar ta ce, “Majalisarmu tana godiya da kokarin shiga tsakani ta hanyoyin dalibai da iyaye da ’yan jarida da kungiyoyin fararen hula da sauransu, wajen magance matsalar.
“Sai dai ASUU a matsayinta na kungiyar mutanen da suka san ya-kamata, tana da hakkokin da gwamnati ya kamata ta girmama.
“A sakamakon haka, mun yanke shawarar tsawaita yajin aikin da mako takwas don ta ba gwamnati dama, ko dalibai sa samu damar komawa makarantu.
“Tsawaitawar za ta fara aiki ne daga karfe 12:01 na safiyar ranar Litinin, 14 ga watan Maris na 2022.”