A kwanakin baya ne aka sanya hannu kan yarjejeniyar Gasar Rubutu ta Aminiya a tsakanin Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya da Gandun Kalmomi da Open Arts da ke Kaduna. A hirarsa da Aminiya Farfesa Ibrahim Malaumfashi wanda shi ne jagoran gasar, ya bayyana yadda za a fara gasar da sauran bayanai game da gasar da ake sa ran za a rika gabatarwa duk shekara:
Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihin gasar rubutu a kasar Hausa?
Malumfashi: To da farko dai gasar rubutun labarai musamman kagaggun labarai na Hausa ba sabon abu ba ne. Domin an fara sanya gasar rubutu tun lokacin Turawan mulkin mallaka a tsakanin 1932 zuwa 1933 da manufar samar da littattafan karatu na Hausa. Ganin cewa a al’adar Bahaushe karya abar kyama ce ballanatana a ce karyar ce za a yi wa kwalliya a sanya ta a cikin littafi har a rika sayarwa abu ne mai wahala. Wannan ya sanya a wancan lokacin aka kasa samar da irin wadannan littattafai har sai da suka yi amfani da hanyar sanya gasa, inda suka sanya wani dan abu da za a bayar, wato kamar kazar karfi ga wadanda suka yi nasara. Hakan ya sanya masana ciki har da malamai suka shiga cikin gasar ta farko wacce ita ta samar da manyan marubuta irin su Abubakar Imam da Bello Kagara da sauransu.
Saboda haka gasa tana sanyawa a samu sababbin marubuta da sababbin littattafan karatu. Haka aka ci gaba da shirya irin wannan gasa an yi a 1978 da 1980 an yi a 1989 sannan daga baya daga shekarar 2006 har kawo yanzu an yi gasa daban-daban wadanda suka taimaka wa rubuce-rubuce.
Aminiya: Me za ka ce game da Gasar Rubutu ta Aminiya da Kamfanin Media Trust da hadin gwiwar Gandun Kalmomi suka shirya?
Malumfashi: Kamar yadda ka fada wannan gasa ce da Kamfanin Media Trust a karkashin Jaridar Aminiya da hadin gwiwar Gandun Kalmomi suka shirya domin samar da wata gasa ta kananan labarai kagaggu a kowace shekara kwatankwacin gasar rubutu ta Hikayata da Sashin Hausa na Gidan Rediyon BBC ke sanyawa a kowace shekara.
Aminiya: Mene ne makasudin gasar?
Malumfashi: Kamar sauran gasannin da suka gabata wannan gasa za a rika yin ta ce don samar da sababbin marubuta da sababbin littattafan karatu wadanda za a rika yin nazarinsu a jami’a da sauran makarantu. Don haka ne mu malaman jami’a musamman ni da kuma Gandun Kalmomi wacce nake jagora muka tuntuba tare da neman shugabannin Kamfanin Media Trust wanda su ne mawallafa Jaridar Aminiya su ba mu wata dama tare da tallafin Open Arts da ke Kaduna don mu samu mu rika shirya gasar rubutu wacce za ta taimaka wa rubutu da marubutan su kansu da kuma sauran al’umma. Kuma alhamdulillahi mun cimma yarjejeniya kuma mun sa hannu za mu fara shirya wannan gasa da muka sanya wa suna Gasar Rubutun Gajerun Labaru ta Aminiya.
Aminiya: Wadanne rukunin marubuta ne za su rika fafatawa a cikin gasar?
Malumfashi: Wannan gasa ta sha bamban da sauran gasanni da muka shirya a baya, domin muna so ne mu ba matasa ’yan shekara 18 zuwa 35 dama su fito da basirarsu. Bugu da kari kuma matasan sun hada da maza da mata ne, ba kamar gasar Hikayata ba wacce mata ne kawai suke yin ta. Sannan wani abin da ya kara bambanta wannan gasa da sauran na baya shi ne a yanzu za mu rika bada maudu’in da za a yi rubutu a kansa ne kowace shekara ba wai mu saki abin sakaka ba kowa ya rubuta abin da yake so.
Aminiya: Wa zai dauki nauyi gasar a yanzu?
Malumfashi: A halin yanzu Gidauniyar Media Trust da Aminiya ce za ta dauki nauyin gasar dari bisa dari kafin nan gaba mu samu wasu manyan kamfanoni ko bankuna su shigo cikin abin su taya su daukar nauyin gasar.
Aminiya:Yaya za a yi da labaran da suka ci gasar?
Malumfashi: A karo na farko dukkan labarai 15 na farko da suka ci wannan gasa Kamfanin Media Trust zai buga su a cikin littafi daya wanda za a sayar kuma a raba ribar a tsakanin Kamfanin Media Trust da su marubutan da kuma bangarenmu na Gandun Kalmomi. Sannan labarai uku na farko da suka ci gasar, a tsarin da muka yi a yanzu za a samu mafassara su fassara su zuwa harshen Ingilishi kuma mu yayata su a duniya don nuna wa duniya irin basirar da Hausawa ke da ita.
Aminiya: Wadanne kyautuka wadanda suka zo na daya zuwa na uku za su samu?
Malumfashi: Gidauniyar Media Trust da Aminiya a karkashin Kamfanin Media Trust ta tanadi Naira dubu 250, ga wanda ya zo na daya sai Naira dubu 150, ga na biyu, wanda ya zo na uku ya samu Naira dubu 100.
Aminiya: Wadanne labarai kuke bukata a aiko da su ?
Malumfashi: Muna bukatar sababbin kagaggun labarai wadanda ba a taba buga su ba kuma muna son ba za wuce kalmomi 1,500 ba, don a ba matasa dama su rubuta gajerun labaran da idan muka hada su a karshe za mu samu cikakken littafi na karatu wanda za a iya nazarinsa a makarantu,
Aminiya: Yaushe za a fara gasar?
Malumfashi: Cikin ’yan kwanaki za a fara ganin sanarwar shiga gasar a Jaridar Aminya da shafinmu na yanar gizo na Gandun Kalmomi da kuma shafin Open Arts na yanar gizo da suaran shafuka na kafafen sada zumunta.
Aminiya: Wane kira kake da shi ga ma’abota rubutu?
Malumfashi: Abin da zan ce musu ga dama ta samu, musamman matasa masu sha’awar rubutu, su zo su wasa kwakwalwarsu su baje kolin basirarsu su rubuto su turo mu kuma mu ba alkalanmu su duba daga nan zuwa wata shida za a fitar da sakamako.
Aminiya: Wane tabbaci za ka ba masu sha’awar shiga gasar na yi musu adalci?
Malumfashi: Wannan tambaya ce mai muhimmanci domin a yadda muka tsara za mu samar da alkalai uku ne. Da farko su kansu alkalan ba za su san junansu ba. Haka duk labaran da za a ba alkali ya duba za a tura masa ne ta imel kuma sai mun cire sunayen wadanda suka rubuta su da lambobin wayarsu. Saboda haka kowane zai duba labaran da suke a wurinsa ya ba su maki, in ya gama ya maido mana. Mu kuma sai mu tattara labaran da alkalan suka ba wa maki daga nan za mu gano wanda suka zaba, a cikin 15 din da suka fi ba wa maki mu kuma za mu zauna mu fid da na daya da na biyu da na uku. Ka ga mu kanmu sai a sannan ne za mu duba mu ga ma wane ne ya rubuta labarin da ya zo na dayan da sauransu. To ka ga babu wata hanya da za a sa wani son kai ko kabilanci ko wani abu makamancin wannan.