Manajan Daraktar Hukumar Tashoshin Ruwa ta Najeriya (NPA), Hadiza Bala Usman ta ce, an kawo karshen babakeren da kamfanin Intels na kula da manyan jiragen da suke kawo man fetur da gas ne domin a inganta gasa a fannin tattalin arziki tare da bayar da ilin da masu bukata za su taka rawa a bangaren.
Shugabar ta bayyana haka ne lokacin da ta kawo ziyara hedkwatar kamfanin buga jaridun Daily Trust da Aminiya da ke Abuja, inda ta ce, kawar da babakeren ya taimaka wa masu harkar da dama kuma ya rage wa masu gudanar da ita tsadar gudanar da harkoki a Najeriya.
Ta yi watsi da tunanin da wadansu ke yi na cewa hana Intels babakeren wani yunkuri ne na rage karfin dukiyar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar kafin zaben shekarar 2019. Ta ce, hatta manyan kamfanonin mai na duniya da suke harka a Najeriya sun koka cewa kebe wani bangare a matsayin tashoshin manyan jiragen dakon man fetur da gas yana kara tsadar harkokin kasuwancinsu.
Ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ya amince cewa duk wata tashar jiragen ruwa tana iya saukar da jirgin dakon man fetur da gas babu batun babakere. Da aka tunatar da ita korafin kamfanin Intels cewa an yi sauyi neba a lokacin da ya kamata ba, sai ta ce, ba haka ba ne, domin a lokacin da aka bayar da hayar tashoshin babu tashar da aka ba ta ikon yin babakere a kan jiragen dakon man fetur da gas. Kamfanin Intels ya samu wannan dama ce daga baya aka rika sauya ka’idar shekara da shekaru kan babakeren na Intels, inji ta.
Hadiza Bala Usman ta ce, an yi tsarin ne domin amfanin tattalin arzikin Najeriya, kuma ba yi adalci ba a jingina lamarin da daidaikun mutane.
Ta ce wani abu da ke kawo matsala a tsakanin Hukumar NPA da kamfanin Intels shi ne batun asusun bai-daya na TSA, wanda ya bukaci a rika mika dukan kudaden hukumar ga asusunta na Babban Banki kafin a fitar don biyan wani hakki, lamarin da ya jefa wa Kamfanin Intels din shakku duk kuwa da cewa ba zai yi asarar wani kudin shiga ba.
Shugabar Hukumar NPA din ta ce tana maraba da binciken da Majalisar Dattawa take yi a hukumar game da kwangilolin tone tashar jiragen ruwa. Ta ce ita ma tana da tunani irin na Majalisar Dattawan kan yawan kudin kan cewa kashe Dala miliyan 150 kan yashe hanyoyin ruwa na Legas da Bonny kawai ga dukkan alamu ba su dace da aikin da ake yi ba. Ta ce Hukumar NPA tana shirin nemo kwararru domin su yi mata nazarin batun yashe ruwa domin hakan ya zama jagora kan kudin da za a rika kashewa a nan gaba.
Hadiza Bala Usman ta ce burinta na jawo karin manyan jiragen dakon kaya zuwa Najeriya ya hadu da cikas, sakamakon matsin tattalin arziki da kasar nan ta shiga da kuma wasu tsare-tsare na gwamnati. Amma ta ce an samu karuwar fitar da kaya zuwa waje musamman kayayyakin amfanin gona da ma’adinai. Kuma ta ce Hukumar NPA tana aiwatar da umarnin Shugaban Kasa domin saukaka gudanar da harkoki ta hanyar hana ’yan daba shiga tashoshin da dakile bayar da cin hanci ga jami’ai da magance cinkoson da ake samu a tashoshin jiragen ruwan.