✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da mayakan ISWAP 104 suka mika waya

Mayakan ISWAP 104 da suka yi saranda sun ce uwar bari suka gani a sakamakon ragargazar da sojoji ke musu ta sama da kasa a…

Mayakan kungiyar ISWAP 104 da suka mika wuya sun ce uwar bari suka gani a sakamakon ragargazar da sojoji ke musu ta sama da kasa.

Karin mayakan kungiyar ta’addancin da suka mika wuya sun bayyana cewa yin hakan ya zame musu dole ne saboda ragarzazar da jiragen yaki da sojojin kasa suke wa maboyarsu.

Mayakan sun bayyana haka ne bayan sun mika wuya tare da iyalansu a ranar Litinin ga rundunar sojoji ta musamman da ke Damboa Jihar Borno.

Hukumomin sojin Najeriya sun bayyana cewa mutanen da suka mika wuya sun hada da maza 22, mata 27 da kuma kamanan yara.

Sun bayyana cewa gargazar da sojojin suka tsananta a kan mayakan kungiyar ce ta tilasta musu fitowa daga mabyarsu da ke yankin Damboa da ke Kudancin Jihar Borno.

A baya-bayan nan, shugabannin soji da na siyasa sun karkatar da hankulansu zuwa yankin Kudancin Borno, a sakamakon yawan hare-haren ta’addancin da ISWAP ke kaiwa a yankin da ya hada da Damboa, Chibok, Askira Uba da sauran wuraren da ke makwabtaka da Tabkin Chadi.

Majiyoyi masu tushe sun shaida mana cewa mayakan na samun sauki kurdawa su koma Dajin Sambisa da Dajin Alagarno bayan sun kai hare-hare a kananan hukumomin da aka ambata.

Idan ba a manta ba a yankin Askira Uba ne mayakan ISWAP suka kai wa ayarin motocin Kwamandan Birged na Musamman na 28, Birgediya Dzarma Zirkushu, suka kashe shi da wasu sojoji uku a watan Nuwamban 2021.

‘Sabon alfijir’

Wata majiyar soji ta shaida wa wakilinmu ranar Litinin da dare cewa dole nan gaba karin mayakan kungiyar su mika wuya, saboda ba su da wani zabi.

“Muna ci gaba da aiki, ina tabbatar maka cewa dole komai ya sauya saboda an riga an shawo kan yawancin abubuwan da ke kawo wa aikinmu tarnaki,” inji majiyar.

Ta ce, “Yanzu lokacin rani ne, ko’ina ya yi fili; Sannan jiragen yaki na Super Tucano da sauran kayan yaki sun riga sun isa yankin Kudanci da kuma Arewacin Borno.

“Yanzu dai, ainihin mayakan da suka mika wuya daga cikin wadannan mutum 104 guda 25 ne, sauran kuma mata ne da kananan yara, wadanda da ma su ke kawo mana jan kafa wurin yi wa mayakan luguden bama-bamai.

“Ba abu mai kyau ba ne a ce mun kashe mutane masu rauni shi ya sa muke daukar lokaci. Amma duk da haka, ga su kana gani suna fitowa daga maboyarsu saboda sun san cewa yanzu ba kamar da ba ne.

“A cikin ’yan kwanakin da suka wuce mun kashe wasu kwamandojin ISWAP musamman a yankin Tabkin Chadi.

“Yadda suke yin dango suna komawa yankin Kudancin Borno ya ragu, saboda luguden wuta da muke ci gaba da yi musu,” a cewar majiyar.

Daga watan Yunin 2021 zuwa yanzu dai daruruwan mayakan Boko Haram da iayalnsu sun mika wuya ga sojojin Najeriya bayan an kashe shugaban kungiyar, Abubakar Shekau, a watan Mayun shekarar.

Kazalika bayan kashe shugaban kungiyar ISWAP, Abu Musab Albarnawi, rikicin shugabanci ya dabaibaye kungiyar, lamarin da ya kai ga rabuwar kai tsakanin mabiya.

Wasu majiyoyi sun ce yawancin manyan kwamandojin kungiyar sun ajiye makamansu, inda wadansu daga cikinsu da suka mika wuya ake ba su horo karkashin shirin sauya tunanin tsoffin ’yan ta’adda ma ‘Operation Safe Corridor.’

A watan Yulin 2021, Rundunar Hadin Kai ta Sojin Najeriya ta karbi mayakan Boko Haram da iyalansu mutum 91 da suka mika wuya a yankin Arewacin Borno.

Daga baya a watan Augusta, Kakakin Rundunar Sojin Kasa, Birgediya Onyema Nwachukwu, ya sanar cewa wasu karin mayaka 56 sun mika wuya.

Sannan a watan Satumba, rundunar sojin ta ce mayaka da kwamandojin Boko Hara tare da iyalansu mutum 8,000 sun mika wuya a cikin watan Yunin shekarar.