✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da ma’aikata suka tsunduma yajin aiki a Neja

Gwamnatin jihar ta yi alkawari yau shekara biyu kenan amma ba ta cika ba.

Ma’aikatan Gwamnati a Jihar Neja sun tsunduma yajin aikin gama-gari biyo bayan rashin biya musu wasu bukatunsu da suka ce gwamnatin jihar ta yi alkawari yau shekara biyu kenan amma ba ta cika ba.

Kungiyoyin Kwadago a Jihar Nejan dai sun shiga yajin aikin ne biyo bayan wasu tarin bukatunsu da suka ce gwamnatin jihar ta gaza cikawa yau shekara biyu ke nan.

Shugaban Kungiyar Kwadago ta NLC reshen jihar, Kwamared Yakubu Garba, ya yi karin haske da cewa, “na farko yau shekara biyu ke nan da gwamnatin jihar Neja ta dakatar da biyan kudin ajiye aiki wato gratuity ga ma’aikatan Kananan Hukumomi da na jihar da suka yi ritaya.

“Na biyu kuma kudade wadanda aka zaftare daga cikin albashin ma’aikata da har yanzu ba a biya su hakkokinsu ba.

“Na uku shi ne akwai kaso 30 cikin 100 na albashin ma’aikata na watan Yunin 2020 shi ma har yanzu babu amo ballantana labarinsa.

Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito cewa yajin aikin ya shafi dukkan ma’aikatan Kananan Hukumomi da na jihar wanda ya kai ga rufe asibitocin gwamnati kamar yadda wani mazauni a yankin Suleja, Haruna Abdulwakil ya bayyana.

Haruna ya ce, “yanzu muna nan Babban Asibitin Suleja, mun kawo marasa lafiya ne, sai kawai ak ce mana ma’aikatan asibitin sun shiga yajin aiki.

“Saboda haka sai dai mu kwashi marasa lafiyan da muka kawo mu kai su asibitin kudi, yanzu ba mu san wani irin hali ake ciki ba.

“Talaka bai da wani ’yanci a yanzu, sai dai mun fawwala wa Allah komai.

Ita ma Gwamnatin Jihar Nejan ta bakin Kwamishinan Yada Labarai, Muhammad Sani Idris, ta ce ta fara tattaunawa da kungiyoyin kwadagon.

Sani Idris ya ce “a tattaunawar da muka yi cikin Yardar Allah ta haifar da da mai ido, domin kuwa akwai abubuwa da bukatu da suka gabatar, kuma an cim ma matsayar wasu daga cikinsu, musamman irin abin da suka shafi kudin ritaya daga aiki, da wannan kaso 30 na albashin da suke ta magana a kai.

“Duk dai wannan a yanzu akwai yarjejeniya da aka kulla a kai kuma mun warware tufkar.

“Yanzu abin da ya rage shi ne za a mu ci gaba da zaman tattaunawa kan abin da ya shafi Kananan Hukumomi.

Bayanai sun ce ajin aikin na gama gari na zuwa ne makonni takwas malaman makarantun Firamare suka shiga yajin aiki a jihar, inda iyaye ke ci gaba da bayyana damuwarsu a kan lamarin kasancewar yaransu na zaune a gida.