Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Zakon Kasa a Najeriya (EFCC) ta alaƙanta yawaitar katsewar lantarki da yadda cin hanci da rashawa suka yi katutu a bangaren samar da lantarki na kasar.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede ne ya bayyana hakan a yayin ziyarar da Kwamitin Yaki da Cin Hanci na Majalisar Wakilai ya kai ofishinsa a ranar Talata.
- Muna buƙatar Dala biliyan 10 a riƙa samun wutar sa’o’i 24 a Najeriya — Ministan Lantarki
- Muna ɗaukar matakan kawo ƙarshen Lakurawa — Minista
Olukoyede ya bayyana cewa bincike ya gano yadda ’yan kwangila suke kawo kayayayyaki marasa inganci.
A makon da ya gabata, manyan biranen Najeriya da suka hada da Abuja, Lagos, da Kano sun fuskanci katsewar lantarki a karo na goma da hakan ta faru a wannan shekarar.
Rashin ayyuka masu inganci
Olukoyede ya faɗa wa kwamitin cewa “A yayin da nake magana a yanzu haka, muna fama da matsalar lantarki. Idan kuka ga wasu daga binciken da muke yi a ɓangaren samar da makamashi, za ku zubar da hawaye.
“Mutanen da aka baiwa kwangila na kawo kayan lantarki, maimakon su yi amfani da gejin inganci na 9.0, sai su sayo masu ingancin 5.0.”
Olukoyede ya ci gaba da bayyana irin rashin inganci a manyan ayyuka da ake gudanarwa, yana mai cewar a shekaru 20 da suka wuce, kasa da kashi 20 na ayyuka ka kammala gudanarwa.
Ya jaddada cewar rashin gudanar da manyan ayyuka na cigaba ya bayar da gudunmawa sosai wajen daƙile Nijeriya ta ci gaba a fannin tattalin arziki.
Badakalar cin hanci
Shugaban na EFCC ya ce a yanzu haka akwai badaƙalar cin hanci da ta’annati ga tattalin arziki 20,000 da ake bincike a kai.
Olukoyede ya bukaci gwamnatin Nijeriya da ta bayar da fifiko ga aiki da gaskiya, keke da keke, da tabbatar da aiki da dokoki don yaki da cin hanci a bangaren makamashin lantarki.
Baya ga rashin ingantattun kayan aiki, ‘yan ta’adda ma na yin zagon kasa ga harkokin samarwa da rarraba lantarki kamar yadda mahukunta suka tabbatar.
A watan da ya gabata, Arewacin ƙasar ya fuskanci katsewar lantarki na sama da kwanaki bakwai bayan da ‘yan bindiga suka lalata hanyoyin rarraba lantarkin, in ji Kamfanin Rarraba Lantarki na Najeriya (TCN).