Alhaji Nura Manu Soro, Kwamishinan Kudi na Jihar Bauchi da ya yi murabus kasa da wata biyu da nada shi dan kasuwa ne mai son ci gaban ilimi. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana daliln da gidauniyarsa ta Nura Manu Soro Foudation ta ware Naira miliyan 100 don biya wa dalibai kudin makaranta daga firamare zuwa jami’a:
An ce gidauniyarka ta ware makudan kudi don biyan kudin makaranta ga dalibai, me ya sa ka yi haka?
Dalilina shi ne ilimi, ginshikin al’umma ne. Kuma na lura ilimi ya lalace a kasar nan. Dalili shi ne in ka lura za ka ga makarantunmu sun lalace, ba waje mai kyau da za a yi karatun, malaman kansu na bukatar a kara ilimantar da su. Abin da zai ba ka takaici shi ne idan yara sun kammala makaranta sai ka ga ba su iya karatu sosai ba. Kuma bayan haka in ka dubi yawan al’ummar da muke da ita sai ka ga mutane kalilan ne suke iya zuwa makaranta. Sha’anin rayuwar yau shi ya sa muka ga cewa yana da kyau a samu tallafi; don in an samu tallafin mutane za su iya tafiya karatu kuma in sun je makaranta wadansu daga ciki za su iya karatun.
Wane tallafi kake bayarwa don dalibai su yi karatu?
Tallafi ne na kudin makaranta kawai wanda za mu biya wa yara. Amma kafin mu biya kudin a kowace makaranta akwai ’yan kwamiti da za su rika binciko mana su rika tantance wadanda suka dace su samu tallafin. Idan aka samo su mu ne za mu biya musu kudin makaranta har su kammala a duk matakin karatun da suke.
Ta wace hanya za ku rika biya?
To ba wai za mu dauki kudi ne mu bai wa mutum ba. Abin da za mu yi idan an tantance cewa wannan dalibi mai hazaka ne kuma iyayensa ba su da karfin da za su biya masa kudin makaranta, za mu karbi lambar asusun ajiyar bankin makaranta da sunan dalibi da lambar da yake ita a makarantar, sai a biya kudin ta banki, shi kuma a ba shi shaidar biyan kudi ta banki, ya kai makarantar.
Cikin shekara nawa dalibi zai ci moriyar haka?
Dalibai za su yi ta cin moriyar kudin har sai sun kare da izinin Allah. Idan kudin sun kare za mu nemo wasu mu sake sakawa har su kammala makarantar. In dai mun ga kudin ya zama yana amfanar da al’umma,
Nawa ka tanada, shirin zai fadada ne ko a cikin kasar nan ne kawai?
Yanzu akwai Naira miliyan 100 da muka tanada, kuma wannan kudi mun tanade shi ne don daliban makaranta da ke karatu a kananan hukumomi 20 na Jihar Bauchi kawai. In akwai marayu a yankin Jama’are ko Ningi ko Warji ko Bauchi ko Ganjuwa ko Katagum ko Gamawa ko sauransu za su iya rubuta sunayensu, a fadi nawa ne kudin makarantarsu, za a biya musu in an tantace su. Kuma kafin yanzu mun tanadi wannan kudi, haka idan akwai a Jami’ar Jiha da ke Gadau su suka fi mu sanin wadanda suka kamata a taimaka musu, za su turo a tantance sai a biya don kungiyoyinsu na makaranta su suka fi mu sanin wanda ya fi dacewa a taimaka masa.
Na lura cewa a Babban Masallacin Kasa da ke Abuja, mutane suna zuwa neman tallafi wajenmu muna yi, sai jami’ai da limaman masallacin in suka ga dalibi suka tantance ya kasa biyan kudin makaranta sai su karbi takardar biyan kudin makarantarsa da lambar asusun banki na makarantar su kawo mana mu je mu biya musu kudin mu dawo musu da takardar shaidar biya su bai wa dalibin ya kai makaranta ya ci gaba da karatu.
Ka ga ba mu san dalibin ba ba mu gan shi ba, ba mu da wata alaka da shi mun taimake shi saboda Allah saboda Annabi. Haka wannan ma duk daliban da za mu tallafawa za mu tallafa musu ne saboda Allah da Annabi ba mu san su ba kuma ba sai mun gansu za mu biya musu kudin makarantar ba. Illa iyaka kwamitin da na fada, in ya tantance ya kawo mana sunayen daliban da suke da su a makarantar firamare ko sakandare ko gaba da sakandare, in mun yi bincikenmu za mu je mu biya musu.
Hatta jami’an da suke kula da wadannan kudi su ma ba za su taba ko sisin kwabo da hannunsu ba; ba za ma su ga kudin ba, daga asusun banki ne zuwa asusun makaranta za a biya kai-tsaye. Ba sai mutum ya taso ya same ni ko ya samu ’yan kwamitin ba. Kuma kowane dan makaranta in dai a Bauchi yake zai ci moriyar tallafin. Kungiyoyin makarantar za su turo mana amma babu ruwanmu da dinkinka na yunifom ko littattafai ko wani abu, mu dai kudin makaranta kawai za mu biya. In dai kana karatun, lallai ne kana da wadancan kayayyakin koyon karatu. Kuma ba makarantun boko kawai ba, mun saka makarantun Sakandaren Musulunci, (HIS) da makarantun Islamiyya, in dai akwai marayun da ba za su iya biya ba za mu iya biya musu.
Ko zuwa yanzu an fara cin gajiyar tallafin?
Eh, gaskiya an fara don mun fara biya wa dalibai tun daga ranar 12 ga watan Mayun bana, kuma zuwa yanzu mun iya biya sama da Naira miliyan 8 da dubu 300, kudin makaranta ga dalibai 314 da suka fito daga Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi da Kwalejin Kimiyya da Koyon Sana’a ta Abubakar Tatari Ali da ke Bauchi da Jami’ar Jihar Bauchi da ke Gadau da Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Tarayya da ke Bauchi.
Wadanne kalubale kuka fuskanta?
Kalubalen da muke fuskanta shi ne gaggawa daga masu neman cin gajiyar shirin. Wani zai zo yana sauri; mu kuma muna da ka’ida sai mun tantance, kafin mu amince a bayar da umarnin fara biya. Kuma koda ka nemi tallafin tilas sai ka bi ka’idojin da aka shimfida, shi ne muke rokon jama’a su fahimta. Haka daliban da suke karatu a wasu jami’o’i na wajen jiha, in dai ’yan asalin Jihar Bauchi ne su ma za su iya cin gajiyar shirin, don haka a zo a nema kuma yanzu za mu kakkafa kwamitocin da za su rika tantance jama’a a dukkan kananan hukumomi 20 na Jihar Bauchi don mu kara kusanto da jama’a yadda za su shiga shirin samun tallafin cikin sauki.
Ka taba yin wani taimako da ya burge ka?
Kwarai da gaske, akwai wanda ya burge ni; ga Barista Abdulwahab na taba taimaka masa ya sayi takardar JAMB ya je ya yi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Abin farin ciki shi ne a shekarar 2017 ya zama dalibin da ya fi kowane kwazo a fannin koyon aikin lauya a jam’iar. Ka ga zamowarsa zakara a makarantar abin farin ciki ne gare mu don ya yi abin da ya kamata.
Ka koka kan rashi da karancin bada tallafi a fagen ilimi; me za ka ce ga wadanda Allah Ya huwace musu?
Na yi ta fada a kullum ni burina a maida tallafa wa ilimi ya zama yayi ko abin da kowa zai rika dokin yi. Kamar yadda za ka ga kowa na da burin gina gida, ya gina masallaci, to tallafa wa ilimi ya zama haka. Haka nake so dukkan al’ummarmu mu rungumi tallafa wa ilimi don in ba a gyara ilimi ba kowa ya gane dama da hagunsa, al’ummarmu za ta ci gaba da tafiya yadda take; to amma in aka gyara ilimi to komai zai tafi daidai.
Kuma muna rokon Allah Ya taimake mu Ya cika mana burinmu don wannan yunkuri da muka yi a samu cikakkiyar nasara. Wanda ya dace su samu, su samu Allah Ya sa su yi karatu su ma in sun fito su yi wa wadansu don a’lummarmu ta amfana.