✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da Dangote da Abdulsamad suka bar masu kudi a baya

Dalilin da Kanawa suka bar masu kudin Najeriya da ma Afirka a baya

Kanawa biyu, Aliko Dangote da Abdulsamad Rabiu, sun yi wa masu kudin Najeriya fintinkau, inda suka samu karin arziki a cikin ’yan kwanakin nan.

Bakano na farko shi ne Alhaji Aliko Dangote, wanda ya ba wa biloniyoyi akalla 406 baya a fadin a duniya, bayan dukiyarsa ta karu zuwa Dala biliyan 19.4 (kimanin Naira tiriliyan 20).

Matsayin Dangote ya daga zuwa mutum na 94 mafi kudi da duniya ne a cikin mako guda, bayan karuwar dukiyarsa daga kimanin Naira riliyan 17 (Dala biliyan 17.1), a cewar mujallar Forbes.

A cikin mako guda kamfanin simintinsa ya samu gagarumin ciniki har hannun jarin kamfanin ya karu daga N319 zuwa N538.80.

A kasa da kwana biyu kamfaninsa na siminti, wanda shi ke da kashi 86 na hannun jarin, ya yi cikinin kimanin Naira biliyan 900 (Dala miliyan 850)

A watan nan na Janairu arzikinsa ya karu da kimanin Naira tiriliyan hudu (Dala biliyan hudu) bayan matatar mansa ta fara aiki.

A halin da ake ciki dukiyar Dangote, wanda shi ne mutum mafi kudi a Najeriya da ma fadin nahiyar Afirka, ta doshi Naira iriliyan 20 (Dala biliyan 19.4), a cewar Forbes.

Mai bi masa a Najeriya, Abdulsamad Rabiu, Shugaban Rukunin Kamfanin BUA, shi ma bakano ne.

Abdulsamad Rabiu ya zama mutum na biyu mafi arziki a Najeriya ne bayan da ya doke attajirin Kudancin Najeriya, Mike Adenuga mai kamfanin yada labarai, wanda ya kasance a masayi na biyu na kwanaki 17 kacal.

Likafar Abdulsamad ta sake dagawa zuwa wannan matsayi ne bayan dukiyarsa ta Dala biliya 5.7 ta karu da kimanin Naira tiriliyan biyu (Kimanin dala biliyan 1.5).

Daga farkon watan Janairun nan da muke ciki, dukiyar Abdulsamad ta karu zuwa kimanin kimanin Naira tiriliyan bakwai (Dala biliyan bakwai).

A ganinkiu ta yaya arzikin Dangote da Abdulsamad zai amfani Kanawa da Arewacin Najeriya.