✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ba zan janye ƙudirin ƙara haraji ba — Tinubu

Tinubu ya yi watsi da shawarar Majalisar Tattalin Arziki kan ƙudirin ƙara haraji.

Shugaba Bola Tinubu ya yi watsi da shawarar Majalisar Tattalin Arziki (NEC) wadda ta nemi ya janye ƙudirinsa na ƙara haraji.

Tun farko dai Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ce ta bayyana adawarta da ƙudirin tana mai cewa ya saɓa wa muradun jama’ar Arewacin ƙasar.

Haka ita ma yayin zaman da ta gudanar a ranar Alhamis, NEC ta ba shawarar jingine ƙudirin ƙara haraji domin buɗe ƙofar tuntuɓar dukkanin masu ruwa da tsaki.

Sai dai cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Juma’a, Tinubu ya buƙaci NEC da ta bari a aiwatar da sabuwar dokar harajin.

Sanarwar wadda ta yaba wa Majalisar Tattalin Arzikin dangane da shawarar da ta bayar, ta kuma tunatar da ita muhimmancin ƙara harajin domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

Dangane da hakan ne Tinubu yake tunatar da duk masu bore a kan ƙudirin da ya riga da aike wa Majalisar Tarayya da cewa har yanzu ƙofar tuntuɓe-tuntuɓe ga masu ruwa a buɗe take.

Sanarwar ta ce shugaban ya ji duka koken da ake yi game da ƙudurin da buƙatar janye shi da ake yi, to sai dai ya ce ƙudirin – wanda tuni aka fara muhawara a kansa a majalisar — ba za a janye shi ba, sai dai ya ce a iya yin wasu gyare-gyare a lokacin muhawarar majalisar da kuma jin ra’ayin jama’a.

Sanarwar ta ƙara da cewa “shugaban ƙasar bai aike da ƙudurin gaban majalisar ba, har sai da ya kafa kwamitin wanda kuma ya yi aiki na tsawon shekara guda yana tattara ra’ayoyi game da ƙudirin daga wajen masu ruwa da tsaki a fannin tattalin arziki daga duka ɓangarorin ƙasar.

“Shi wannan ƙudiri da ke gaban majalisa, an aika shi domin kawo gyara a fannin yadda ake tafiyar da karɓar haraji a ƙasarmu.”