✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ba zan bai wa Gwamnatin Tinubu shawara ba — Sarki Sanusi

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce ba zai bai wa Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kowacce shawara da sunan taimako ba dangane da…

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce ba zai bai wa Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kowacce shawara da sunan taimako ba dangane da halin da ƙasar ta tsinci kanta ta fuskar tattalin arziki.

Sarkin ya bayyana haka ne a yayin taron tunawa da fitaccen lauyan nan ɗan gwagwarmaya, Chief Gani Fawehinmi karo na 21 a Legas.

Ya ce, zai iya yin tsokaci kan wasu batutuwa da suka shafi Nijeriya da hasashen abin da zai iya faruwa da kuma shawarar yadda za a iya kaucewa hakan.

Sai dai a cewarsa, ba zai yi hakan ba, domin muddin ya ba da wata shawara tamkar ya taimaki gwamnatin ta Tinubu ce kuma a halin yanzu ba shi da niyyar taimakonta.

Sarki Sanusi II ya ce ya yanke shawarar ba zai yi kowane irin tsokaci a kan tattalin arziki ko sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa ba, “saboda idan na yi bayani hakan zai taimaki gwamnatin, to amma ba na son na taimaki gwamnatin nan.”

Ya kara da cewa, “lallai abokaina ne amma da zarar abokanka sun daina ganin kima kuma suka juya ma baya, ni ma ba zan ɗauke su kamar abokai ba.

“Saboda haka a yanzu zan koma gefe na zuba ido dangane da ababen da ke faruwa tamkar ina kallon wani fim na nishaɗi domin ita kanta ba ta da mutane masu kima da za su zo su yi bayanin abin da gwamnatin take yi ba.

“Sai dai zan faɗi abu guda ɗaya wanda shi ne ina da yaƙinin cewa mafi rinjayen kaso na matsalolin tattalin arziki da ƙasar nan ke fuskanta sun samo asali ne tsawon shekaru da dama da suka gabata.

“Kazalika, ko shakka babu akwai kura-kurai da gwamnatin Tinubu ke tafkawa wajen aiwatar da manufofi da sauye-sauye a ɓangaren tattalin arziki.”

Ana iya tuna cewa dangantaka ta yi tsami tsakanin Sarki Sanusi da gwamnatin Tinubu tun bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mayar da rawanin Sarautar Gidan Dabo wadda tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tuɓe masa.