Festus Keyamo, Babban Lauyan Najeriya (SAN), ya bayyana dalilin rashin ganin sunansa a jerin lauyoyin da za su kare nasarar Asiwaju Bola Tinubu, zababben shugaban kasa a kotu.
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, amma manyan abokan hamayyarsa sun garzaya kotu domin kalubalantar sakamakon zaben.
- DAGA LARABA: Wane Ne Bola Ahmed Tinubu? Bayani Daga Dattawan Legas
- Buhari ya gana da mahaifin Sarkin Qatar a Doha
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, na Jam’iyyar PDP da Peter Obi na Jam’iyyar LP sun yi ikirarin cewa kowannensu ya lashe zaben.
A safiyar ranar Talata ne sunayen lauyoyi 48 da za su tsaya wa Tinubu suka karade kafafen sada zumunta.
Sai dai jam’iyyar APC mai mulki ta fitar da jerin sunan mutum 12 na manyan lauyoyin da za su kare nasarar Tinubu a kotu.
Sai dai wani abun mamaki sunan Keyamo ya yi batan-dabo a ciki.
A wani martani da ya mayar kan rashin ganin sunansa, Keyamo ya ce: “Ga masu tambaya, kundin tsarin mulki bai bayar da damar minista mai ci ya shiga cikin wata kungiyar lauyoyi masu zaman kansu ba.
“Amma zai iya tallafa wa tawagar game da shirye-shiryenta.
“Don haka, ministocin da suke da matsayin SAN za su iya shiga cikin tawagar lauyoyin bayan ranar 29 ga watan Mayu.”
Keyamo ya taka rawa sosai a yakin neman zaben Tinubu, inda ya kasance mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC.
A halin yanzu shi ne minista a ma’aikatar kwadago da samar da ayyuka.