A cikin shekara 95 a duniya, Alhaji Tanko Yakasai ya ga dimbin abubuwan ci gaban sabuwar Najeriya: ba gani kadai ba, har ma ya shiga an dama da shi.
Jigo a Jam’iyyar NEPU, kwamishina a tsohuwar Jihar Kano babban dan jam’iyya a Jamhuriyya ta Biyu , Yakasai ya tuno wasu daga cikin wadannan abubuwa a tattaunawarsa da gidan talabijin na Trust TV.
- Kira ga Shugaban Kasa Buhari
- Yadda muka ji labarin yakar ’yan bindiga da sojoji ke yi — Mutanen Sakkwato
A tattaunarwar Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana ra’ayinsa kan wasu al’amuran kasa kamar yadda Aminiya ta nakalto:
Akasarinmu ba mu kai shekara 95 ba. Yaya kake ji da ka kai wadannan shekaru?
Ni a wurina ba wani bambanci, sai dai a ce na ga abubuwa da dama da suka faru da wadansu ba su gani ba. Baya ga wannan game da lafiyata da damar yin magana da sauransu ina jin komai daidai.
Mutane da dama sun ce tsufa aba ce mai wahala; shin kai kana jin wahalar?
Eh; akwai abubuwan da ban iya yi. Nakan yi saurin manta abu. Amma abin da nake jin dadi shi ne nakan iya tunawa da shi cikin kwana daya ko mako ko wata ko a shekara.
Mene ne dadin tsufa, me yake cikin tsufa da kake tunanin matasa ba su sani ba da suke iya rasawa?
Lokacin da muke yara babu rediyo ko talabijin, amma muna jin dadin rayuwarmu ta yin wasu ayyuka kamar wasanni da zuwa makaranta da musayar ra’ayi da sauraren labarai daga dattijai da sauransu.
Ba mu yi tunanin abin da yake faruwa yanzu zai faru ba. Mutane da dama sa’annina suna mamakin abubuwan da suke faruwa a yanzu.
Kamar me; wadannen abubuwa ne suke ba ka mamaki?
Misali, abu zai faru a Amurka ko Rasha ko wani sashi na duniya cikin kankanin lokaci ka ji shi ko ka kalle shi ko ma ka hadu da shi, ya kara maka fahimta da ilimi.
Muna da cikakken lokaci a baya amma ba irin wannan dadi na sanin abubuwa da dama a dan kankanin lokaci ba.
Wannan baiwa ce ta musamman daga Ubangiji da ya wajaba mu gode maSa.
Wani muhimmin abu game da kai, shi ne da dan ilimin zamani kamar yadda muka fahimta, ka zama jagoran wata jam’iyya ta kasa, ka zama kwamishina ka zama mashawarcin Shugaban Kasa, ta yaya ka cimma haka?
Babu bambanci wajen koyo a jami’a da koyo a gida. Mun fara koyo a gida. Mun halarci makarantar allo, amma galibin ilimin zamani da na samu na koye shi ne a gida da cikin gari.
Wadanda suka samu ilimin zamani a makarantu sun ji dadin samunsa ta hanya mai sauki fiye mu. Amma ina jin mu da muka koya ta hanya mai wahala mu ma mun samu abin da zai tabbata a jikinmu da za mu yi saurin tunawa.
Ta yaya ka iya bunkasa ka iya sarrafa harshen Ingilishi da sanin harkokin duniya?
Na fara ne kwatsam a matsayin dan jarida a 1953 da jaridar The Comet a matsayin wakili daga baya na zama Editan Hausa.
Na zama Sakataren Watsa Labarai na Kasa na jam’iyyata NEPU kuma na yi gasa da wadanda suka samu ilimi sosai, wadanda suka taimaka min wajen fitowa ta yadda zan iya hulda da su yadda ya kamata.
Akwai kalubale amma gaskiya ina farin ciki da na cije a haka; amma ba abu ne mai sauki ba.
Kafin haka kai tela ne, yaya kaiya sauyawa?
Dinki shi ne sana’a mafi kyau; ba wai don ina tela ba, a’a saboda babu wanda bai cin gajiyar dinki: sarakuna, janar-janar, farfesoshi da kowa.
Ba za ka je aji a matsayin farfesa ba, sai ka sanya sutura, tela ne ya mayar da kai abin sha’awa.
Idan za ka yi aure za ka bukaci ado, haka idan za ka bayyana a talabijin irin wannan, za ka so a gan ka cikin ado, dukkan wadannan ayyukan tela ne.
Sai dai abin takaici mutane kalilan ne suka fahimci muhimmanci da matsayin teloli ga dan Adam, saboda babu wanda zai ce babu ruwansa da sana’arsu.
Na fara sana’ar dinki ne a 1941 lokacin da na dawo daga makarantar allo daga Bauchi. Na fara koyon dinki ne a garin Hardawa da ke Misau a Jihar Bauchi, na zama kwararre lokacin da na dawo.
Abin da muka fi dinkawa, Wudiya a yanzu ba a damu da ado da ita ba. Wundiya wani nau’in babbar riga ce da ba kowane tela ne zai iya dinka ta ba, in kuma ba za ka iya dinka ta ba, ba za ka samu abokan harka ba.
Amma yanzu babu mai tunaninsu, ba a bar sha’awa ba ce gare ku, haka ni ma saboda ba ni da Wundiya a yanzu.
Bari mu dubi batun shigarka NEPU; ga alama ka fuskanci matsala sosai a dangantakarta da jagoran NEPU, Malam Aminu Kano, duk da cewa kowa a jam’iyyar na kallonsa a matsayin jagora. A wani lokaci an taba korarka daga jam’iyyar daga baya aka dawo da kai. Me ya faru?
Wani abin sha’awa shi ne abin da ya faru da ni a daukacin tarihin jam’iyyun siyasa a Najeriya, ina jin ni kadai ne dan jam’iyya da aka kora kuma aka dawo da ni.
Me ka yi aka kore ka?
Wani abokina ne ya gayyaci ni zuwa Tarayyar Sobiyet da China a 1960. Na tuntubi Malam Aminu Kano; cewa ina son mu tafi da wadansu shugabannin NEPU, saboda an nemi in zo tare da shugabannin jam’iyya.
Bai so haka ba, amma na riga na yanke shawarar zuwa. Don haka sai na nemi wadansu shugabannin NEPU da kaina wadanda suka amince su je tare da ni.
Muka tafi Legas kwana daya kafin ranar samun ’yancin kan Najeriya.
Na zauna da Malam Aminu Kano washegari da safe muka dauki hayar bas ta kai mu Accara daga can muka shiga jirgi zuwa Mali daga can kuma sai Mosko daga can sai Beijing.
Mun shafe kusan wata uku muna zagaya wurare a China daga baya Tarayyar Sobiyet daga Tarayyar Sobiyet zuwa Jamus ta Gabas.
To lokacin da na dawo, Malam Aminu Kano bai ce komai ba, amma wadansu ’yan jam’iyyarmu ba su ji dadin zuwa na Rasha da China ba, saboda babban abin kunya ne a je Rasha da China.
Don haka suna ganin na aikata wani abu da zai hada NEPU rigima da Turawan mulkin mallaka, kuma ga shi yanzu muke samun ’yancin kai.
Saboda wannan wadanda ba su ji dadi ba daga ’yan jam’iyya, bayan tattaunawa da Malam Aminu Kano, suka yanke shawarar a kore ni ba tare da an bukaci in kare kaina ba.
To lokacin da suka kore ni, sai na yanke shawarar ba zan koma wata jam’iyya ba, maimakon haka sai na kafa wata jam’iyya mai suna Jam’iyyar Sawaba ta Najeriya (SPN).
Sai muka kulla abota da Jam’iyyar Sawaba ta Jamhuriyyar Nijar, wadanda suka dauki makami suna gwagwarmaya.
Gwagwarmayar makami a Nijar?
Ba ka san an yi haka ba? Eh, an yi; Jam’iyyar Sawaba ta yi amfani da makamai a gwargwamayarta a Nijar domin kwatar ’yancin Nijar daga Faransa.
Sun yaki mulkin Faransa, amma ba mu yi haka a Najeriya ba, kuma ina jin tsoron yiwuwar kwaikwayarsu ce ya taka rawa wajen sa abokan siyasarmu su ce a kore mu daga jam’iyyar.
Kai dan Kwaminis ne?
Ni cikakken dan gurguzu ne mai bin koyarwar Markasanci, kuma har yanzu haka nake. To saboda cewa akwai wannan rarrabuwa a jam’iyyar sai aka kore ni tare da mutanen da suke kusa da ni.
Don haka lokacin da na kafa Jam’iyyar Sawaba, wadanda aka kora sai suka biyo ni muka fara yada ta.
A lokacin wadansu shugabannin NEPU sun hango hadarin kyale Jam’iyyar Sawaba ta yadu saboda za ta raunana karfin NEPU, kuma ga shi taken NEPU shi ne “Sawaba” sai suke jin kada a bari mu yi alaka da magoya bayan NEPU, domin akwai yiwuwar mu janye su zuwa Jam’iyyar Sawaba, wadda za ta iya bice hasken NEPU a wurin jama’a.
Sun fahimci hakan ya sa mun samu karbuwa a wurin jama’a sai su da kansu suka yanke shawarar su maido mu cikin NEPU.
Sojoji sun yi juyin mulki a 1966 kuma kai da fitattun ’yan NEPU kun shiga gwamnatin har ka zama kwamishina. Yaya za ka kare haka a matsayinka na mai kokarin kwato ’yancin talakawa amma yanzu kun shiga gwamnatin soji har ka zama kwamishina?
Bayan juyin mulkin an samu yunkuri a Arewa da ya hado ’ya’yan jam’iyyu daban-daban; NEPU da NPC da UPE da MBC da sauransu.
Mun yi aiki tare wajen adawa da gwamnatin Janar Aguiyi Ironsi wadda take yaki da ’yan siyasa.
Mun hada kai wajen adawa da gwamnatin Ironsi, kuma wannan kokari da muka yi ne muka samu goyon bayan da ya karya gwamnatin.
Don haka lokacin da Laftanar Kanar Yakubu Gowon ya zama Shugaban Kasa sai ya nada fitattun ’yan adawa a gwamnatinsa a matakin kasa kuma ya umarci gwamnoni su yi haka a jihohi.
To sai aka nada ’yan NEPU da hatta MBC a matsayin Kwamishinonin Tarayya (ministoci). Mutane irin su Malam Aminu Kano da Shettima Ali Monguno da Shehu Shagari daga NPC.
A Kano, ina cikin mutanen da aka zabo mu don zama kwamishinoni; tare da sauransu kamar Sani Gezawa wanda shi ne Sakataren NPC. Wannan shi ne yadda muka shiga gwamnati.
Gwamnatin tana neman goyon bayan kowane bangare na al’umma, kuma mun ba ta goyon baya, sun ji dadin haka suka saka mana da mukamai.
Na fahimci dalilin nada ka a matsayin Kwamishinan Watsa Labarai, yaya aka yi ka zama Kwamishinan Kudi?
To kafin in zama Kwamishinan Watsa Labarai, ni ne Sakataren Watsa Labarai na jam’iyyata; wanda kusan irin aikin daya ne.
Lokacin da Kwamishinan ’Yan sanda Audu Bako ya zo a matsayin Gwamna da ya zo nada kwamishinoninsa, ya tuntubi mutane da dama bisa umarnin Gowon, kuma daga cikin mutanen da ya tuntuba akwai Malam Aminu Kano.
Malam Aminu kuma ya ba da sunayen mutane da yawa wadanda suke wakiltar bukatun Kano, NPC da NEPU da ’yan kasuwa da sarakuna da sauransu.
To mu 10 aka nada, ni aka zabe ni in wakilci bukatun ’ya’yan NEPU, Sani Gezawa ya kare bukatun ’yan NPC, saboda shi ne Sakataren yanki na NPC, Aminu Dantata ya wakilci ’yan kasuwa.
Sai kuma aka yi garambawul ga kwamishinonin aka tura ni Ma’aikatar Bunkasa Jin Dadin Jama’a da Jam’iyyun Gama-Kai da ma mene ne ba zan iya tunawa ba; ma’aikatu uku aka hada a ka ba ni.
Na yi shekara biyu ina tafiyar da su kafin a ce in rike Ma’aikatar Kudi.
Kwamishinan Kudi, shi ne Alhaji Umaru Gumel. Ya hadu da rashin lafiya ya tafi jinya a Landan. Ya ba da sunana in yi masa riko. Ban sani ba, ina jin Gwamna ya ji dadin aikin da na yi, abin bakin ciki, sai Alhaji Umaru Gumel ya rasu.
To sai Gwamna ya ce in ci gaba da zama Kwamishinan Kudi.
Amma kamar shigarka Ma’aikatar Kudi ta taimaka wajen matsalar da ka samu lokacin da aka rusa gwamnatin Audu Bako, bayan hawan mulkin Janar Murtala Mohammed. An gudanar da bincike tare da kwace kadarori, kuma kana cikin wadanda aka kwace kadarorinsu. Ka kare kanta sosai a littafin tarihinka; ta yaya ka mallaki wasu daga cikin kadarorin, wannan shi ne abin da mutane suke magana a kai. Kana ganin gwamnati ta yi gaggawar yin bincike da kwace kadarorin ne?
A’a. Ka gani, lokacin da Audu Bako ya zo Kano a matsayin Gwamnan Soji ya yi tuntuba sosai.
Ya gamsu sosai da irin shawarwarin da Malam Aminu Kano ya ba shi, don haka ya fi karkata ga shawarwarin Malam Aminu a kan shawarwarin da sauran mutane suka ba shi.
Akasarin mutanen da ya nada ya dauko su ne daga sunayen da Malam Aminu Kano ya bayar. Malam Aminu Kano da Murtala da Inuwa Wada dangi ne, sun fito ne daga zuriyar Fulanin Gyanawa da ke Kano, sai dai Inuwa Wada dan APC ne, ya taba zama Sakataren Tsare-Tsare na APC daga baya ya zama minista da sauransu.
To lokacin da Malam Aminu Kano yake jagoran NEPU da aka kirkiro jihohi kuma saboda sabaninsu tun a Jamhuriyya ta Farko, mutanen da Malam Aminu Kano ya ba da sunayensu sai aka rika ganin sun fi karkata ga NEPU fiye da NPC.
Don haka kimanin mutum hudu zuwa biyar daga cikinmu suka fi kusa da Audu Bako.
To hakan bai yi wa abokan hamayyarmu a NPC dadi ba saboda ana ganin Audu Bako ya fi karbar shawarwarin mutanen da Malam Aminu Kano ya bayar.
Saboda ni ne Sakataren Watsa Labarai na Kasa na NEPU, ni ne fitaccen dan NEPU a kwamishinonin. Don haka duk wata kiyayya a kan NEPU, take karewa a kaina, wannan shi ne dalilin da ake nuna min kiyayya.
Ke nan tunanin kana cikin masu almundahana a gwamnatin Bako…?
An bincike mu, kuma abin da zai ba ka mamaki shi ne ba a gayyaci ni don in kare kaina ba har aka gama binciken; ba ni kadai ba Sani Gezawa ba a gayyace su ba, amma aka kwace kadarorinmu, kuma wadansu daga cikinmu da aka kwace musu kadarorin daga baya an ce su biya wasu ’yan kudi su karbe su.
Akwai alamar kai ma kamar akasarin ’yan Najeriya kana tunanin illar gwamnatin Murtala ya fi alfanunta. Duk da ka amince da wasu nasarorinta, ka ce ya yi kyau ga kasar da gwamnatin ba ta dade ba. Mene ne dalilin wannan hukunci?
Lokacin da aka yi wa Gowon juyin mulki an shigo da abubuwa marasa dadi a siyasar Arewa.
A karon farko rarrabuwa a tsakanin Musulmi da wadanda ba Musulmi ta bayyana a Arewa.
Murtala ta yiwu ka sani, ta yiwu ba ka sani ba, an sa shi a soja ne ta ofishin kawunsa Inuwa Wada, don haka ya fi kusanci da Inuwa Wada fiye da Aminu Kano.
Don haka ina jin wannan ne dalilin ba ni kadai ba ne hatta Malam Aminu Kano ya hadu da wasu kuntatawa. Abin da kawai ya bambanta, shi babba ne a kasa kuma an fi saninsa a kaina.
Don haka akwai tsoron in aka rika yi masa wulakanci irin yadda aka yi min, za a samu martani mai yawa ga gwamnatin. Saboda haka ba ma dasawa da Murtala Mohammed. Ban san shi ba. Ban taba sanin Murtala ba, amma lokacin da aka samu rikici a kasar nan, lokacin da ’yan Arewa mazauna Legas suka tura wani rukuni a tara kudi a Kano; wannan ne lokaci na farko da na ji labarin Murtala Mohammed.
Matashi ne kasa da ni, babu wata alaka a tsakaninsa da ni. Amma yana ganina a matsayin wani mutum da ya fito daga rukunin ’yan siyasar da yake jin ba su kaunar wanda yake so Inuwa Wada, don haka ya ga ya dace ya rama ta hanyar kuntata min da sauran wadansu kalilan da suke rukuninmu.
A matakin kasa, me kake ji game da shi; kana jin wasu daga cikin tsare-tsaren da ya kawo a kankanin lokacin da yake Shugaban Kasa suna da kyau ga kasar?
Ni dan siyasa ne a koyaushe. Ina hukunci ga mutane ne a kan gudunmawar da suka bayar ga al’umma. Ba na son in soki Murtala, amma abin da Murtala ya yi, shi ne kama mutane da daure su da bincike.
A tunanina bai yi wani abin kirki ga Najeriya ba. Ban ga wani abu da wani zai yi magana cewa Murtala ya ba da gudunmawa ga inganta Najeriya da jin dadin mutanenta ba a ra’ayina har zuwa gobe.
Don haka kamar yadda na ce, yana kusa da Inuwa Wada saboda haka yana daukar kansa dan-a-mutum NPC ne, kuma a matsayina na Sakataren Watsa Labarai na NEPU, wani abu ne daban.
Ina jin haka ne ya sa na zama wanda ake hantara da ki a tsakanin mutanen da suke ganin kansu a matsayin cikakkun magoya bayan NPC ciki har da Murtala Mohammed.
Ka taka rawa a gwamnatin NPN da Shehu Shagari ya jagoranta a matsayin wakilin Shugaban Kasa a Majalisar Dokoki ta Kasa. Me ya sa gwamnatin ta gaza?
Wannan batu ne na ra’ayi. Ba na jin gwamnatin ta gaza. Gwamnatin tana da dimbin makiya. Shehu Shagari ba mutum ne mai bushasha ba, don haka akwai ’yan Arewa da dama da ba su jin dadinsa.
Suna cewa ya cika tafiyar hawainiya, suna so ya rika yi kamar na Murtala; ya kama mutanen da suka yi ba daidai ba da sauransu.
Bai yi haka ba. Don haka akwai ’yan Arewa da suke ganin Shehu Shagari ba irin shugabannin da ya kamata su shugabanci Najeriya ba ne, amma mutane irina ina aiki ne bisa ka’ida.
Har zuwa yau Shehu Shagari ne mutum mafi gaskiya. Ya rike ma’aikatu; ma’aikatu uku dabandaban tun daga Jamhuriyya ta Daya har zuwa mika mulki ga farar hula.
Ya rike ma’aikatu fiye da kowane dan Najeriya, idan bai cancanta ba, ba za a ba shi rikon ma’aikatu daban-daban a gwamnatoci daban-daban ba. Farko a gwamnatin farar hula, sannan zamanin soji.
Ya fara a matsayin Kwamishinan Ilimi na Jihar Arewa maso Yamma, sannan saboda kokarinsa aka nemi ya maye gurbin Obafemi Awolowo, lokacin da Awolowo ya yi murabus a matsayin Kwamishinan Kudi na Tarayya (minista).
Gaskiya a tunanina ka fara a matsayin kwamishina a jiha sannan a kai ka Gwamnatin Tarayya a matsayin minista ba karamin yaba wa gaskiyarka ba ne.
Wannan shi ne halin Shehu Shagari. Amma a matsayin dan siyasa, dole ka yi fama da makiya; harka ce ta samun abokai da makiya.
A cewarka ba a yi masa adalci ba ke nan wajen gazawar Jamhuriyya ta Biyu?
A’a; Jamhuriyya ta Biyu ba ta gaza ba. Wadanda suka so kwace mulki ne suka ce ta gaza, amma ba ta gaza ba. Ba a ba ta lokaci ba.
An mika mulki ne shekara 13 bayan ‘tsoma bakin’ sojoji, don haka ba za ka sa ran shugaban farar hula ya rika abu irin na Shugaban Kasa na soja wajen yin abubuwa ba.
Shehu Shagari mutum ne mai sanyin hali; mai taka-tsantsan, amma mutane suna son ya yi gaggawa irin Murtala, sai hakan ba ta samu ba.
Bai yi farin jini a wurinsu ba. Yaya kake jin muna yin abubuwa yanzu sama da shekara 20 na mulkin dimokuradiyya?
Muna da abin da ake kira da Hausa da zabo-kaji, wato ba zabuwa ba ba kaza ba. Wannan shi ne abin da yake faruwa.
A yau ba cikakken mulkin farar hula muke yi ba. Kada ka manta sojoji sun tsoma baki a sa Olusegun Obasanjo ya zama Shugaban Kasa a 1999, kuma ya tafiyar da mulkinsa ne akasari sabanin na farar hula duk da cewa an zabe shi ne.
In ka tuna shi soja ne tun balagarsa; don haka ba za ka sa ran ya sauya hali ba. Haka lamarin yake ga Muhammadu Buhari wanda Shugaban Kasa ne na soja yanzu kuma na farar hula.
Wasu daga cikin dabi’unsa sun fi dacewa da na soji fiye da na farar hula a tsarin dimokuradiyya.
Wannan dabi’a ce; ba za ka tafiyar da akasarin rayuwarka a wata harka ba, kwatsam ka canja yadda kake zuwa wata.
A yau in ka ba ni yadinka zan iya dinka maka, saboda na iya dinkin tuntuni. Abin da kawai ba zan iya ba, shi ne dinkin zamani, amma in ka ba ni tsohon yayi zan iya dinka maka.
To lokacin da mutane suka saba da wani salon rayuwa, canja su zuwa wani wuri, za ka ga suna yin abubuwa irin yadda suke yi a baya.
Shin ka gamsu cewa gwamnatin tana magance matsalolin kasar nan yadda ya kamata?
Zan iya cewa eh ta wani bangaren, amma abin da ya faru shi ne; idan ka dubi abin da Buhari yake yi, yana daukar shawarwari, amma inda nake sukar Buhari shi ne ya nemi mulkin nan sau uku amma bai samu ba. Sai daga baya sa’a ta zo masa ya yi nasara a karo na hudu.
A ra’ayina mutumin da ya yi takara sau uku yana neman shugabancin kasar nan, lokacin da ya samu ya kamata a ce a shirye yake.
Amma tun daga farko na damu saboda tsawon lokacin da Buhari ya dauka kafin ma ya nada Sakataren Gwamnati wanda ba ya bukatar tantancewar kowa. Za ka iya yin sa kana gadon barcinka.
Haka sauran nade-naden mukamai da dama sun dauki wata uku zuwa hudu kafin ya yi. Wannan ya nuna maka bai shirya ba. Sai yanzu ne idan ka dubi tsare-tsaren da yake gudanarwa za a ga suna da kyau, kamar gyara harakar sufurin jiragen kasa.
Da a ce ya fara da wuri da yanzu muna cin gajiyar sufurin jiragen kasa sosai a kasar nan da sauran abubuwan da yake yi a yanzu. To amma lokaci ba ya jiran kowa.
Yanzu yana da sauran shekara daya da rabi ne wa’adin mulkinsa ya kare, kuma zuwa badi warhaka mun shiga batun zabe, hankalin kowa zai koma kan gwamnatin da za a kafa.
Ko gwamnatinsa za ta yi ta fama ne don kammala wasu ayyukan da ta faro. Don haka Buhari yana yin abin da zai iya, amma da ya faro tuntuni da sakamakon ya zama daban.
Shin yana tuntubar fitattun ’yan siyasa irinka?
Ka san ina sukarsa tun farkon gwamnatinsa, kuma shi mutum ne da ba ya yafiya. Don haka baya ga ni ko wadanda ba sa sukarsa mutum nawa daga cikin tsofaffin ’yan siyasa ya jawo a gwamnatinsa?
Ya kamata ya samu wadansu daga cikin irinmu ba ma a ministoci ba, koda a masu ba shi shawara kuma ya rika tuntubarsu lokaci-lokaci.
Mutane irin su Ayo Adebanjo da Nbazuruke Amaechi da sauransu, suna nan, wadansu ma suna kasa da shekaruna.
Amaechi yana tare da Buhari kwanaki kadan, ban sani ba, me kake tunani kan alamar da ya nuna ta alkawarin zai duba batun sakin Nnamdi Kanu mai son kafa kasar Biyafara, saboda akwai ayarin da ya je wurinsa lokacin da ya yi alkawarin zai duba yiwuwar yin afuwa? Shin ya yi wani alkawari ne? Ya ce zai yi dubi a kai. Ban sani ba, kana ganin wani abu ne da za a…?
Ina da shakka idan Shugaban Najeriya ko kowace kasa zai kawar da kai daga wani mutum da ya ayyana yaki da kasarsa; ba ma ayyana yaki kadai ba, har ma da kai hare-hare a kan jami’an tsaro yana kashe sojoji da ’yan sanda da sauransu.
Buhari shi ne Shugaban Kasa. Yana da ikon ya yafe wa duk wanda ya so; ba ni da ikon da zan hana shi, amma ba zan yi haka ba idan ni ne shi. Ba zan yafe ko in afuwa ga wanda ya ayyana yaki a kan wannan kasa ba.
Ni cikakken dan kishin kasa, na yi yaki don kasar nan na je kurukuku lokuta da dama domin kasar nan, wadansu mutane su fito su ayyana yaki da kasar nan; abin daga hankali ne.
Wane abin kirki ne Nnamdi Kanu ya yi wa Najeriya ko ga kabilar Ibo?
Ba shi ya kawo Biyafara ba, ya iske Biyafara ce, yana karami lokacin da aka ayyana Biyafara. Don haka ya rage ga Shugaba Buhari. Mutanen da Nnamdi Kanu yake nuna wa kiyayya akasari ’yan Arewa ne; musamman Hausawa da Fulani.
Ni ba Bafulatani ba ne’ ni Bahaushe ne. Don haka ba ni da ikon hana Buhari yin afuwa ga Nnamdi Kanu. Yana da ikon ya yi, amma ba zan goyi bayansa ba.
Shin ka damu da wadannan yunkuri, Biyafara, Kudu maso Yamma da sauransu, inda abokin tasowarka Ayo Adebanjo a bayan nan yake cewa ba su amince da 2023, don haka a dakatar da shirin a kira wani taron kasa?
Da Ayo Adebanjo da ni mun yi aiki a Taron Tsarin Mulki da Janar Abacha ya kira. Ayo bai kai dukkan wadannan batutuwa ga taron ba kuma shi ne lokaci mafi dacewa da Ayo zai bayar da gudunmawarsa. Bayan haka bai wadatar ba a yi kiran a sake fasalin kasa.
Me zai hana Adebanjo ya bayyana abin da yake nufi da sake fasalin kasa? Ai yana yi a duk lokacin da ya samu dama. Yana cewa mu koma ga Tsarin Mulkin 1963?
Ya san hakan ba za ta sabu ba; babu wanda zai mayar da jihohi 36 zuwa jihohi uku a Najeriya; koda shugaban soji ne.
Lokacin da wani yake kiran a yi wani abu, zai yi kyau ka yi tunanin yiwuwar wannan abu; shin zai yiwu ko yana fadi ne saboda neman goyon bayan matasa wadanda ba su san illar abin da yake kiran a yi ba? Ina jin babban abin da yake nema akalla a koma ga taron da Jonathan ya kira a shekarar 2014?
To ai sai ya fadi haka.
Yana cewa ne akalla takardun da aka gabatar su zamo tushe, ba ka ganin hakan ya wadatar?
A’a; ni ba haka na fahimci yana nema ba. Yana neman a sake fasalin kasa ce, da aka matsa ya yi karin bayani sai ya fara wata magana ta daban.
Wannan fa wani gogaggen lauya ne mai shekara 93 yana da sama da shekara 60 da fara aikin lauya. Ni ba lauya ba ne, amma ina ji sosai zuwa yanzu zan iya gabatar da rubutacciyar bukata koda ba za a yi aiki da ita ba, akalla wata rana mutane za su karkade ta su fara duba ta; bai daddale wannan matsayi ba, bai mika jadawalin yadda za a sake fasalin Najeriyar ba.
Ni dan siyasa ne na san abin da ’yan siyasa za su ce don kawai su yi suna. Na san abin da mutane za su ce wanda zai yiwu kuma a aiwatar.
Mene ne matsayinka kan karba-karbar mulki?
Ban san masu son tsayawa takarar ba tukuna, amma na amince da matsayar NPN. Ni dan kwamitin zartarwa ne kuma mataimakin shugaban reshen jam’iyyar na Kano, na yi wa NPN aiki daga farko har karshe.
Ina daya daga cikin wadanda suka daddale tsarin shiyya da jujjuya mulki a NPN tare da mutane irin su Umau Dikko. Don haka ina goyon bayan shiyya-shiyya da karbakarba. Amma ina ganin ya yi sauri a fara nuna daidaikun mutane duk da cewa ba su fito sun bayyana ba.
A bari ’yan siyasar su fara nuna sha’awarsu su gabatar da shirye-shirye da suka tanada ga kasar nan. Zan fi son in goyi bayan wanda yake da kyakkyawan abu ga kasar maimakon kirari. Ba na son kirari.
Kana cewa ba za ka goyin bayan wanda bai cancanta ba a kan tsarin karba-karba…? Babu abin da za ka iya a kan haka.
Abin da yake faruwa a yanzu shi ne a zahiri muna bin tsarin jam’iyyu biyu ne. Kuma ba na ganin yiwuwar jam’iyyun biyun su gabatar da ‘’yan takara daga sashi daya na Najeriya; za a zo, amma ya dogara da dan takarar da aka gabatar daga Arewa da daya daga Kudu bisa tsare-tsaren da za su zo da su game da kasa da nake da su, don inganta wannan kasar.
A littafin tarihin rayuwarka ka fadi wani abu mai ban sha’awa; cewa za ka iya rubuta littafi a kan tataburzarka a kan aure. Akwai labarin da ke yawo kan yadda aka ba ka matar aure da ba ka so ka yi tawaye na shekara hudu daga baya wani aure ta. Me za ka iya cewa a kan wadannan abubuwa?
Na rubuta a littafin, Allah Mai matukar taimako ne, Allah Ya san yadda na sha wuya a farko kuma cikin rahamarSa Ya biya ni.
Ina da ’ya’ya 19 yanzu a raye kuma sun fito ne daga matan da na aura, na yi auren ne bayan aurena na farko da na biyu.
Dukkansu suna da digiri ko digiri na biyu, wadansu ma digiri na uku. Ni ba mai kudi ba ne, ban dauki nauyin kowanensu zuwa jami’a ba.
Sun yi aiki wurjanjan ne kuma yanzu suna cin gajiyar iliminsu. Don haka Allah Ya biya ni ta hanyar ba ni matan da nake so suke sona, kuma za ka ji mamakin jin cewa matar da na aura a karshe tana da ’ya’ya biyar da ni, kuma sun haifa min jikoki 12 ko 13; hakan ya kawo ina da jikoki kusan 60.
Tataburzar da na samu a aure daga farko ba shirina ba ne. A lokacin galibi samari ana aurar musu ’yan matan da ba su suke zaba ba, iyayensu ne suke yanke shawarar wadanda za su aura ko a’a. A nawa bangaren Allah Ya sauya min kuma ina farin ciki da haka.