✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilan da za a fuskanci karancin fetur na wata 6 a Najeriya —IPMAN

Gwamnatin Tarayya ta ware Naira tiriliyan 3.6 domin biyan tallafi zuwa Yunin 2023.

Kungiyar Dillalan Man Fetur a Najeriya (IPMAN), ta ce za a ci gaba da fuskantar karancin fetur a fadin kasar har zuwa watan Yunin wannan shekarar.

Kungiyar ta ce wahalhalun ko karancin na da alaka da shirin Gwamnatin Tarayya na janye tallafin mai baki daya a karshen watan Yuni.

Mai magana da yawun IPMAN na kasa, Cif Ukadike Chinedu, ya shaida wa Jaridar Punch cewa shigo da mai daga ketare da kokarin gwamnati na janye tallafin sun jefa ’yan Najeriya cikin wahala.

Ya ce, “Wannan batu na tallafi da shigo da man fetur daga kasashen waje, su ne manyan dalilan da suka sa muke fama da wannan matsalar ta karancin man fetur.

“Wannan matsalar za ta tsawaita har sai gwamnati mai ci ta bar mulki a watan Mayu ko kuma har zuwa watan Yuni na wannan shekara.

“Haka kuma dabdalar canjin kudi tana shafar shigo da man fetur, shi ma ya sa farashin man fetur din ya yi tsada.

“Takardun kudi na naira sun yawai yayin da kuma Dala ta yi karanci.

“Don haka mafita ita ce mu tace danyen mu a nan, mu samu ma’ajiyar mu ta yi aiki.”

Ya kara da cewa, “Har ila yau, ya kamata mu lura cewa mafi akasari, duk lokutan da wata gwamnati za ta bar mulki, yawanci ana samun karancin man fetur. Hakan ya faru ko a lokacin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan.

Tun a shekarar da ta gabata al’ummar kasar ke fama da karancin mai a sassa daban-daban na Najeriya, musamman a Arewa.

A ranar Litinin, Ministan Albarkatun Fetur, Timipre Sylva, ya ce kamfanin mai na NNPC na tafka asara kan farashin da ake sayar da man a yanzu.

A makon da ya gabata, Ministar Kudi da Tsare-Tsare, Zainab Ahmed, ta ce Gwamnatin Tarayya ta ware Naira tiriliyan 3.6 domin biyan tallafi zuwa Yunin 2023.