Kullum sai kara samun matasa da suka iya taka leda a Arewacin Najeriya ake yi, amma yawancinsu gwanancewar tasu kan kare ne a kwallon layi ko kuma su yi tashe na dan lokaci.
Daga zamanin da ake kiran kungiyar kwallon kafa ta Najeriya da Green Eagles zuwa yanzu da ta koma Super Eagles, yawan ’yan Arewa, musamman Hausawa a cikin tawagar sai kara raguwa yake yi.
- Na biya Ladin Cima N40,000 a fim din Gidan Badamasi —Nazir Salihi
- Kourt Zouma na fuskantar shan dauri saboda marin kyanwa
A makon jiya ne aka kammala Gasar Cin Kofin Afirka a kasar Kamaru, wadda kasar Senegal ta lashe bayan ta doke takwararta da Masar a bugun fanareti.
A tawagar Super Eagles da ta je gasar, akwai ’yan Arewa guda biyar: Ahmed Musa da Zaidu Sanusi da Simon Moses da Sadiq Umar da Jamilu Collins.
Sai dai duk da haka, Hausawa guda uku ne kacal a cikinsu: Zaidu, Sanusi da Ahmed Musa. Sai dai rauni ne ya hana Shehu Abdullahi halartar gasar domin an gayyace shi.
Idan ana batun zaratan ’yan kwallon Najeriya, tun a da zuwa yanzu, ’yan asalin Arewa Hausawa wadanda akalla suka buga Gasar Cin Kofin Afirka ba su wuce 11 ba kacal.
An yi dan wasa Anas Ahmad da Shafiu Mohammed wadanda ’yan wasan fitacciyar tsohuwar kungiyar kwallon kafa ta Racca Rovers ce ta Jihar Kano, wadda ta yi fice sosai a tsakanin shakarun 1978 zuwa sama.
Anas ya buga Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka ta shekarar 1978, shi kuma Shafiu ya buga ta shekarar 1980, inda Najeriya ta lashe gasar a karon farko.
Shafiu yana cikin wadanda suka lashe gasar a matsayin dan wasan gaba.
Wadanda aka fi sani
A Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka ta 1984, an samu ’yan asalin Arewa Hausawa guda biyu da suka buga — Ibrahim Mohammed da Ali Baba. Sai Abdul Aminu da ya buga gasar a 1990 da 1992.
Akwai kuma wadanda aka fi sani, irinsu Garba Lawal wanda ya fi kowane dan Arewa fice da dadewa yana jan zarensa. Garba Lawal ya buga Gasar Cin Kofin Afirka a 2000 da 2002 da 2004 da 2006.
Sannan akwai ai Tijjani Babangida wanda ya buga ta 2000 da 2002, sai Sani Kaita da ya buga ta 2006 da 2010.
Sauran ’yan wasa irinsu Dahiru Sadi da Sale Lato da sauransu sun taba buga wa Najeriya, amma ba su taba zuwa Gasar Cin Kofin Afirka ba, ballantana Kofin Duniya.
A jerin gasannin da Najeriya ta lashe na Cin Kofin Afirka, sau biyu ne kacal aka ci da Hausawa a ciki.
Ta shekarar 1980, an lashe da Shefiu Mohammed, sai ta shekarar 2013 da aka lashe da Ahmed Musa wanda dan asalin Jos ne na Jihar Filato.
Hausawa a tawagar Super Eagles ta yanzu
A yanzu haka a cikin tawagar ta Super Eagles akwai irinsu Shehu Abdullahi da ke kwallo a kungiyar Omonia ta Cyprus, wanda kuma dan Jihar Sakkwato ne, duk da cewa bai samu halartar Gasar Cin Kofin Afirkar ba.
Sai kuma kyaftin din Super Eagles na yanzu, Ahmed Musa da kuma Zaidu Sanusi wanda dan asalin Jihar Kebbi ne kuma a yanzu haka yana taka leda ne a kungiyar FC Porto ta Portugal.
Akwai kuma Sadiq Umar wanda dan asalin Jihar Kaduna ne, kuma yanzu haka yake taka leda a kungiyar Almeria ta Spain.
Sai dai ana tababa kan asalin Ahmed Musa, kuma bai taba cewa uffan ba kan lamarin. Wasu na ce dan asalin Jihar Edo ne, wasu kuma na cewa dan Jos ne.
Sai dai zance mafi kusanci shi ne dan asalin Jos ne, inda aka haife shi, a wani kaulin kuma an ce mahaifinsa dan Kano ne, mahaifiyarsa ce ake tababar kasancewarta ’yar Jos din ce ko Edo. Bari dai mu bar wannan magana mu karasa batun da muka dauko.
Wadannan nan dai su ne Hausawan da ake tsammanin za a kira a wasan Super Eagles na gaba da za su fafata da Ghana a wasan raba gardama na shiga Gasar Cin Kofin Duniya.
’Yan kasa da 17 da 20
Idan ana batun matasan ’yan kwallo, musamman duba da yadda ’yan asalin Arewa ke taka leda a gasannin ’yan kasa da shekara 17 da ’yan kasa da shekara 20 da ma Olympic, za a ga cewa akwai kwarewa a tattare da su, amma kuma sai su kasa kai bantensu.
Akwai matasan ’yan kwallo da suka buga gasar ’yan kasa da shekara 17 da 20 da Olympic irin su Alhaji Gero da Usman Mohammed da Aminu Umar da Musa Mohammed da Lukman Abdulkareem da Rabiu Ali da Musa Yahaya da sauransu.
Musamman Musa Mohammed wanda har kyaftin ya yi, da Musa Yahaya wanda a Gasar Cin Kofin na ’yan kasa da shekara 17 da Najeriya ta lashe a shekarar 2013 a Dubai aka rika muhawara kan wanda ya fi iya taka leda a cikin shi da Kelechi Iheanacho da Taiwo Awoniyi. Sai dai yanzu su biyun suna Super Eagles, amma shi babu labarinsa.
Haka nan akwai ’yan wasa Hausawa da suka faro da kyau a wasannin ’yan kasa da shekara 17 da 20, amma cikin kankanin lokaci sai a daina jin duriyarsu, amma sai a ga takwarorinsu a manyan kungiyoyin duniya da kuma tawagar Super Eagles.
Dalilan da ke dakile ’yan wasan Arewa
Rashin manyan ejan
A wata tattaunawa da ya yi da Daily Trust, tsohon dan wasan Najeriya, Dahiru Sadi, ya ce akwai matsalar rashin ejan da za su zakulo ’yan wasa a lungu da sakon Arewa.
“Misali, ejan a Kudu zai iya kashe wa matashin dan kwallo kudi har zuwa Naira miliyan daya ko biyu domin ganin yaron ya samu shiga.
“Amma a Arewa saboda N100,000 kawai za a iya cire yaro, saboda ejan din ba ya so ya biya, su ma iyayensa ba za su biya ba ko da suna da kudin.
“Ba su san cewa kasuwanci ba ne mai kyau harkar. ’Yan Kudu sun fi wayewa sosai a wannan bangaren”, inji Dahiru Sadi.
A lokuta da dama idan manyan ejan din kwallo suka zo daga kasashen waje sukan taru ne a jihohin Kudu, ko kuma a Abuja, inda ake buga wasannin gwaji domin daukar ’yan kwallo a fitar da su kasashen waje.
Amma sau tari ’yan wasa daga jihohin Katsina da Kano da Sakkwato da Zamfara ba za su iya zuwa ba, watakila saboda rashin kudi.
Rashin zuba jari
Wani lamarin da ke kawo wa harkar kwallon kafa tarnaki a Arewa shi ne yadda attajiran yankin ba su fiye zuba jari ba a harkar, ko da yake yanzu sun fara farkawa.
A Kudu akwai manyan masu kudi da ke sa kudadensu su bude kungiyoyin kwallon kafa, suna daukar nauyin matasa suna buga kwallon.
Suna ciyar da ’yan kwallon, su ba su kayan wasa da lura da lafiyarsu. Amma da wuya ka samu irin hakan a Arewa.
Halin ko-in-kula
A Kudancin Najeriya, matasa da dama sun dauki kwallon kafa ne a matsayin sana’a, kuma iyayensu sun amince da hakan.
Amma a Arewa yawanci matasan sukan yi kwallo ne a boye, kasancewar yawanci iyayensu ba sa so.
Hakan ke sa ko da an bukaci a yi tafiya da yawo domin wasannin gwaji, ba zai iya fada ba a gida.
Ko kuma idan masu horar da su sun zo har sun fada wa iyayen, sai iyayen su ki amincewa.
Irin wannan ma yakan hana manyan ejan zuwa saboda tsoron kada su kashe kudi, a hana yaron tafiya.
Dahiru Sadi ya ce, “Hausawanmu suna da halin ko-in-kula, inda ba sa nuna damuwa da dagiya a harkar.
“Misali, na taba kai wani matashin dan kwallo kungiyar Lobi Stars ta Makurdi. Har an kammala komai jira kawai ake yi a fara wasanni, kawai muka hadu da shi ya dawo Kaduna.
“Da na tambaye shi sai ya ce min mahaifiyarsa ce take gini, shi ne ta ce masa ya dawo ya lura da aikin.”
Shin za ta canja zani?
Lura da yadda lamarin yake a yanzu, inda Hausawa sukan yi tsokacin cewa ba sa ganin ’yan yankinsu, da kuma yadda aka fara samun sauyi a harkokin kasuwancin ’yan kwallo a Afirka, za a iya cewa da alama gaba za ta fi baya kyau.
Akwai zaratan ’yan kwallo da dama da yanzu suke jan zarensu a kasashen Turai, kuma idan suka ci gaba a haka, nan gaba kadan za a gan su a Super Eagles.