✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilan da suka sanya Buhari bai sanar da majalisa tafiyarsa Birtaniya ba

Aminiya ta gano cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai sanar da majalisar tarayya a rubuce cewa zai yi balaguro zuwa kasar Biryaniya ba.   A zaman…

Aminiya ta gano cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai sanar da majalisar tarayya a rubuce cewa zai yi balaguro zuwa kasar Biryaniya ba.
 
A zaman da majalisar ta yi jiya, Shugaban Majalisar Bukola Saraki ya karanta wasiku hudu wadanda shugaban kasar ya aike wa majalisar amma babu wasikarsa ta tafiya Birtaniya a ciki.
 
A baya Buhari ya rika sanar da majalisar dukkanin baraguron da ya rika yi  a rubuce kamar yadda  sashen na 145 karamin sashen na 1 na kundin dokokin Najeriya ya tanada.
 
Shugaban ya bar Najeriya a ranar Litinin zuwa kasar Birtaniya kuma zai ci gaba da kasancewa a can har zuwa ranar 20 ga watan Afrilu.