Shugaban gidan dambe na kasuwar Alaba Rago da ke Jihar Legas, Alhaji Aminu Bature Kucere, ya ce sun dakatar da gudanar da wasan dambe ne saboda ya gundiri masu kallon sa.
Alhaji Aminu Kucere, dan asalin karamar Hukumar Tsafe da ke Jihar Zamfara, ya bayyan wa Aminiya a karshen makon da ya gabata cewa yana shirya wasannin gargajiya don dadadawa jama’a.
Ya ce ‘dalilin da ya sa muka dakatar da wasan dambe shi ne jama’a sun gaji da shi kuma suna bukatar canji. To sai muka kafa kwamiti inda muka tattauna da masoyanmu masu kallon wasannin da muke shiryawa a nan sai muka cimma matsaya a kan mu dakatar da shi mu koma yin wasan dabe wanda ake kira dirama na gargajiya kafin wani lokaci. Mu da ma muna shirya wasanni ne don nishadantar da masu kallonmu. Duk wasan da suke so shi muke shiryawa ba ma shirya wasanni haka kawai sai mun shawarci jama’a’.
Ya ci gaba da cewa ‘Tuni wasannin dabe sun yi nisa a gidan sannan kuma mutane suna ci gaba da nuna gamsuwarsu da yaba mana kan kokarin da muke yi. Mun gayyato fitattun kuma kwarrarun ’yan wasan fim don burge ’yan kallo. Mutanen da ba sa zuwa a da sun dawo yanzu suna zuwa kallon wasan dirama. Yanzu gidan yana cika makil’.
Ya bayyana cewa yanzu hankulan jama’a ya karkata ne zuwa kallon wasan dabe ko kuma dirama a Legas.
‘Shi ya sa ka ga mu ma mun karkata akalar wasanninmu zuwa wasannin da za su kayatar da jama’a tare da tabbatar da cewa kudin da jama’a suka biya ba su tafi a banza ba kuma mun kayata filin wasan, mun sake masa fasali, mun yi masa fenti da zane-zane irin na zamani tare da tsaftace shi da samar da wutar lantarki da kuma samar da tsaron lafiyar jama’a’. Inji shi.
Aminu wanda ya shafe shekaru fiye da 12 yana shirya wasan dambe a kasuwar Alaba ya bayyana cewa zai dawo da wasan duk lokacin da jama’a suka bukaci ya yi hakan.
Dalilan da suka sa muka dakatar da wasan dambe- Aminu Kucere
Shugaban gidan dambe na kasuwar Alaba Rago da ke Jihar Legas, Alhaji Aminu Bature Kucere, ya ce sun dakatar da gudanar da wasan dambe ne…