✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilai uku na sauke Sufeto Janar Mohammed Adamu

Zargin almundahana da gazawar aiki da halascin karin wa'adin zamansa a mukamin

Aminiya ta gano hakikanin dalilan da suka sa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sallami Shugaban ’Yan Sanda Najeriya, Mohammed Adamu, kwana 28 kafin cikar wa’adin aikinsa da Buharin ya kara masa.

Kwararan majiyoyi masu kusanci da lamarin sun bayyana wa Aminiya, ’yan sa’o’i bayan maye gurbin Mohammed Adamu da DIG Usman Alkali Baba cewa an yi hakan ne domin tseratar da mutucin gwamnati bayan faruwar wasu abubuwa.

Karkatar da kudade

Majiyarmu a Ma’aikatar Harkokin ’Yan Sanada ta ce wani rahoton da Daily Trust ta wallafa kan badakala a Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ya yamutsa hazo a Fadar Shugaban Kasa inda ta nuna fushinta ga Ma’aikatar da kuma Shugabancin Rundunar.

Rahoton ya fede biri har wutsiya kan yandda aka kyale Kwamishinonin ’Yan Sanda na Jihohi da Shugabannin Manyan Ofisoshin ’Yan Sanda su yi ta kansu wajen samar da kayan gudanar da aiki.

Wakilanmu sun kuma gano cewa ba a biyan jami’an ’yan sanda da ake turawa su gudanar da ayyuka na musamman alawus dinsu; Hatta kudaden gudanar da ofisoshin ’yan sanda, gagarar samuwa suke yi.

An kuma gano cewa a duk zarge-zargen ana dora laifin ne a kan Shugaban Rundunar, Mohammed Adamu.

“Akwai rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa ranar Asabar wanda ya fallasa yadda rashin samar da isassun kudaden gudanar da harkokin ’yan sanda da kuma gazawar shugabanci a bangaren suke gurgunta  harkokin ’yan sanda a Najeriya; hakan kuma babban abin kunya ne ga gwamnati,” inji majiyarmu ta Ma’aikatar Harkokin ’Yan Sanda.

Harin Imo

Majiyar ta ce ana cikin hakan ne ’yan bindiga suka kai wani kazamin hari da Hedikwatar ’Yan Sanda ta Jihar Imo, da sanyin safiyar Litinin, wanda ya kara fama gyambon.

Kasancewar aikin ’yan sanda ne samar da tsaro da kuma tabbatar da doka da oda a cikin kasa ya sa masu hankoron darewa a kujerar suka bazama wajen neman kamun kafa, suna bayyana gazawar Mohammed Adam.

A haka ne Ministan Harkokin ’Yan Sanda wanda ya ba da shawarar nada Alkali a matsayin Shugaban Rundunar, ya samu amincewar Shugaba Buhari daga London, inda yake ganin likita cewa ya sanar da sabon nadin.

Shari’ar kara wa Adamu wa’adi

Dama can akwai karar wani lauya, Maxwell Okpara, ya shigar gaban Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja yana kalubalantar karin wa’adin da Buhari ya yi wa Mohamed Adamu.

A makon gobe ne kotun za ta yanke hukunci, kuma alamu sun nuna gwamnati za ta sha kaye a zaman kotun da ke tafe a ranar 16 ga watan Afrilu.

Tun bayan karin wa’adin da Buhari ya yi masa ake ta surutai, yayin da ake ta muhawara game da dacewa ko akasin hakan a doka.

A lokacin dai Gwamnatin Tarayya ta ce an yi hakan ne domin samar da isasshen lokacin zabo wanda zai gaji kujerar.

Yadda aka sallami Mohammed Adamu

Mohammed Adamu ya samu labarin sauke shi ne bayan saukarsa a Abuja daga Imo, inda ya je gane wa idanunsa irin barnar da maharan haramtacciyar kungiyar IPOB, mai karajin neman kafa kasar Biafra suka kai.

Minista Dingyadi ya sanar da sallamar tasa ne ranar Talata a Fadar Shugaban Kasa, ba tare da Shugaba Buhari ko Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo na nan ba.

Da zuwansa, ya wuce zauren ’yan jarida ya sanar da su nadin DIG Alkali, lamarin da ya ba wa wasu ’yan Najeriya da makusanta a Fadar Shugaban Kasa mamaki, musamman yadda ake ganin Buhari na dasawa da kuma yabon Adamun.

Dingyadi ya ce Buhari ya dauki matakin ne bisa tanadin Sashe na 7, karamin Sashe na 2 na Dokar Aikin Dan Sanda (2020) bayan la’akari da girman matsayi, kwarewa da kuma cancanta.

A cewarsa, hakan na daga cikin yunkurin Shugaban Kasa na yin sauyi a bangaren tsaron Najeriya da zumman magance matsalolin da ke addabar kasar.

Dalilin zabo Alkali

Ya ce za a gabatar da sabon nadin ga Majalisar Shugabannin Kasa da za a gudanar nan gaba domin amincewa, kuma Buhari na umartar sabon Mukaddashin Shugaban ’Yan Sandan ya tashi haikan wajen tabbatar da aminci da tsaron rayuka da dukiyoyi a Najeriya.

Ya yaba wa Mohammed Adamu bisa kwarewarsa da jajircewa da kuma kishin da ya nuna a lokacin aikinsa, tare da yi masa fatan alheri.

“Bayan zuzzurfan binciken neman nada Shugaban ’Yan Sanda daga cikin masu mukamin DIG da AIG karkashin Sashe na 7, karamin Sashe na 2 na Dokar Aikin Dan Sanda (2020);

“Bayan la’akari da girman matsayi, kwarewa da kuma cancanta, Shugaban Kasa ya amince da nadin Usman Alkali Baba, PSE, FDC ya zama Mukaddacin Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, nan take,” inji Dingyadi.

Dalilin katse wa’adin Adamu

Game da dalilin kin barin Adamu ya karashe wa’adin wata uku da aka kara masa, Dingyadi ya ce, “Shugaban Kasa na sane da hakan kuma huruminsa ne; shi ke da ikon nadawa ko kara wa’adi ko sallama.

“Yanzu kuma ya yanke shawarar nada wani. Saboda haka, a bar shi da aikinsa, tunda ba hurumin wani ba ne.”

Daga: Sagir Kano Saleh, Abdulaziz Abdulaziz, Muideen Olaniyi, John C. Azu da Idowu Isamotu

%d bloggers like this: