Tun bayan da aka sassauta dokar zaman gida a Yankin Babban Birnin Tarayya da jihohin Legas da Ogun saboda dakile cutar coronavirus, rahotanni daga kafafen yada labarai da dama sun nuna yadda jama’a suke yi wa dokar kariya da aka sanya karan tsaye.
Shugaba Muhammadu Buhari dai ya sanar da sassauta dokar a jawabinda ya yi wa ‘yan kasar inda ya zayyana amfani da kyallen rufe fuska da ba da tazara da tsafta da dokar fitar dare daga karfe 8:00 na yamma zuwa karfe 6:00 na safe da kuma dakatar da tafiye-tafiye tsakanin jihohi a matsayin matakan kariya daga yaduwar cutar.
Duba ga yadda ake kin bin wadannan matakai ne gwamnatin tarayya ta yi barazanar sabunta dokar zaman gidan idan har hakan ya ci gaba da faruwa.
- Za a hukunta duk wanda ya taka dokar hana fita a Filato
- Dokar hana fita: ‘Zaman gida ba abinci ba abin so ba ne’
- COVID-19: Buhari ya roki ’yan Najeriya su zauna a gida
Dalilai biyar da zasu iya sanya gwamnati sake kakaba dokar zaman gida sun hada da:
- Karan tsaye ga matakan kariya
Hukumomi sun bayyana cewa, matakan kariya da suka hada da amfani da kyallen rufe fuska da bada tazara tsakanin jama’a da dakatar da tafiye-tafiye tsakanin jihohi suna da gagarumar rawa da zasu taka wurin dakile yaduwar cutar.
Duk da haka jama’a suna ci gaba da yin harkokinsu ba tare da kulawa da matakan ba, a wuraren da cutar tayi kamari da suka hada da Legas da Abuja.
An kuma zargi ma’aikatan tsaro wadanda aka rarraba saboda tabbatar da dokar da kawo ci baya wurin kiyaye matakan. Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a ranar Alhamis ya koka da cewa, ma’aiktana tsaron suna kawo koma baya a tabbatar da dokar tafiye-tafiye tsakanin jihohin.
- Karuwar wadanda suka harbu
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) a ranar Alhamis ta rawaito karin mutane 381 da suka harbu da cutar. Hakan shi ne mafi yawa da kasar ta samu a cikin kwana guda. Wannan kuma yana zuwa ne kwanaki bayan da gwamnati ta sassauta dokar zaman gida.
Karin da aka samu zai iya tilasta wa gwamnati sake duba yiwuwar maida dokar idan har aka alakantar da hakan ga sassauta dokar.
- Ra’ayin Kwararru
Tuni dai kungiyar likitoci ta kasa tayi watsi da sassauta dokar da gwamnati tayi inda suka bayyana cewa, Shugaban Kungiyar ya rattaba hannu, kungiyar ta bayyana sassauta dokar a matsayin matakin gaggawa da zai iya jawo karin yaduwar cutar.
A nata bangaren, hukumar lafiya ta duniya tayi gargadi akan sassauta dokar a kasashe saboda zai iya jawo hannun agogo baya.
- Yankunan Karkara
‘Yan Najeriya da suke rayuwa a yankunan karkara da ma wuraren da ake samun cunkoso suna fuskantar babbar barazana idan cutar ta shiga yankunansu. Cutar wadda tuni ta fara yaduwa a yankunan masu kananan karfi ta barazanar maida hannun agogo baya a yaki da cutar.
An dade dai mazauna yankunan karkara suna fama da rashin kayayyakin kiwon lafiya. Saboda kaucewa kazantar abubuwa gwamnati tana iya sake duba yiwuwar dawo da dokar.
- Rashin nasarar dokar killace kai
A ranar Alhamis, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa dokar da ta zayyana na cewa kowa ya killace kansa na kwanaki 14 saboda tabbatar da ko suna dauke da cutar bai samu karbuwa ba.
Hakan yasa ta sanya dokar killacewar ta zama dole akan duk wanda zai shigo kasar. Yawancin wadanda aka tabbatar suna dauke da cutar a karon farko dai sun shigo Najeriya ne daga kasashen cutar tayi kamari.
Hakan yasa sun shafawa mutane da yawa wanda hakan ne ya ruruta wutar yaduwar cutar.