✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Dalilai 14 da suka sa Manchester United ta kori Dabid Moyes

Da yawa daga cikin magoya bayan kulob din Manchester United ba su san takamaiman dalilan da suka sanya kulob din ya yi waje rod da…

Da yawa daga cikin magoya bayan kulob din Manchester United ba su san takamaiman dalilan da suka sanya kulob din ya yi waje rod da kocinsa Dabid Moyes a ranar Talatar da ta wuce ba.  Don haka ne muka kalato wasu daga cikin dalilan kamar haka:
1.  Ta tabbata kulob din Manchester United zai gama kakar wasa ta bana a gasar rukunin Premier na Ingila ne da maki mafi karanci a tarihin rayuwar kulob din.
2. Kulob din Manchester United ba zai halarci gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai a kakar wasa mai zuwa ba a karon farko tun bayan shekarar 1995 kimanin shekara 19 da suka gabata.
3. Wannan ita ce shekarar da kulob din Manchester United ya kasa tabuka abin-a-zo-a-gani tun shekaru goma da suka wuce.
4. An doke kulob din sau uku a jere a kakar wasa ta bana, kamar yadda ya taba faruwa da kulob din a shekarar 2001.
5. An fitar da kulob din a gasar cin kofin kalubale na Ingila (FA) a zagaye na uku.  Haka ta taba faruwa ne da tsohon koci Aled Ferguson  sau daya a tsawon zamansa a kulob din.
6. Wannan shi ne karon farko da kulob din Swansea ya samu nasara a kan na United a tarihin kulob din.
7. A karon farko rabon da kulob din Newcastle United ya doke na United tun a shekarar 1972
8. A karon farko rabon da kulob din West Brom ya doke United tun a shekarar 1978
9. A karon farko rabon da kulob din Stoke City ya doke United tun a shekarar 1984
10. A karon farko da aka jefa kwallo a ragar United a kasa da minti daya da fara wasa a gasar rukunin Premier na Ingila wacce Eden Dzeko na kulob din Manchester City na Ingila ya jefa a ragar United a kakar wasa ta bana.
11. A karon farko rabon da kulob din Manchester City da na Liberpool su samu nasara a kan na United gida da waje a tarihin gasar Premier ta Ingila.
12. A karon farko rabon da kulob din Eberton ya doke na United gida da waje tun a kakar wasa ta 1969 zuwa 1970.
13.  A karon farko rabon da kulob din Eberton da na Liberpool su samu nasara a kan United gida da waje a gasar rukunin Premier sai a kakar wasa ta bana.
14. A karon farko da kulob uku Eberton da na Manchester City da kuma na Liberpool su samu nasara gida da waje a kan na United a tarihin gasar Premier na Ingila.