✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalibi ya yi doguwar suma bayan yi masa bulala 6,000

Malamin ya sa karti sun tale yaron a kan tebur, sannan ya rika zabga masa dorina

Wani malamin makarantar allo ya yi wa wani almajirinsa bulala 6,000 saboda zargin akaita sata a garin Ilorin, Jihar Kwara.

Ruwan tsumagiyar da malamin yi wa dalibin da kuma munanan raunuka da ya yi wa yaron a jikinsa sun sa dalibin yin doguwar suma.

Kafin a yi wa yaron bulalar, sai da malamin ya sa karti biyar suka tale shi a kan wani tebur, sannan ya shiga zabga masa dorina, kuma bai tsahirta ba sai da aka yi wa yaron bulala 6,000 a matsayin haddin satta.

Dalibin wanda shi kadai mahaifiyarsa ta haifa, ta sanya shi a makarantar ce a shekarar da ta gabata saboda ya samu ilimin Alkur’ani a wurin malamin wanda dan asalin garin na Ilorin ne.

Aminiya ta samu rahoton cewa, tuni malamin ya yi layar zana bayan da ya samu labarin cewa an kai karar sa wurin Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Jihar.

Wakilin hukumar, Barista Ahmed Rufai, ya shaida wa Aminiya cewa an kwantar da yaron a wani asibiti a Karamar Hukumar Ilorin ta Yamma, da ke jihar.

Ya ce gwamnati da jami’an tsaro sun baza komar farautar malamin.