✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalibin da ake zargi da kwakule wa budurwarsa idanu ya zama ‘kurma’ rana tsaka a kotu

Sai dai lauya mai shigar da kara ya bayyana abin a matsayin wasan kwaikwayo.

An gurfanar da wani dalibin Jami’ar Jos da ke Jihar Filato mai suna Moses Okoh a gaban babbar kotun Jihar ranar Litinin, bisa zarginsa da kisan budurwarsa mai suna Jennifer Anthony.

Dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Alex Muleng, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin, mai kimanin shekara 22, ya kashe budurwar tasa ce mai kimanin shekara 20 a duniya ranar 31 ga watan Disambar 2021.

Mai shigar da karar ya kuma ce daga bisani wanda ake zargin ya kwakule mata idanu.

Insfekta Alex ya kuma ce Moses ya yaudari budurwar tasa don ta halarci wani fatin bikin sabuwar shekara, inda ya kwace wayar salularta ya lalata, ya yi amfani da kafar shi wajen buga kanta a kasa, sannan ya kwakule mata idanu da cokali mai yatsu.

Dan sandan ya ce Moses ya cika wandonsa da iska, kafin daga bisani a cafke shi ranar 15 ga watan Janairun 2022 a Jihar Binuwai.

Sai dai lokacin da aka karanta masa tuhume-tuhumen da ake yi masa, sai ya yi shiru.

Tun da farko dai, lauyan wanda ake karar, N.E Jesse, ya shaida wa kotun cewa wanda yake karewa na fama da matsalar kwakwalwa, saboda haka ba zai iya magana ba.

Sai dai mai shigar da kara ya soki lamirin lauyan, inda ya ce akwai takardar asibiti da ta tabbatar da cewa Moses lafiyarsa kalau, a gaban kotun.

Insfekta Alex ya ce tun kafin ya gurfana a gaban kotun, ya sha yin magana da ’yan sanda da iyalansa da kuma lauyansa, inda ya bayyana matakin kin yin maganar da wasan kwaikwayo.

Alkalin kotun, Mai Shari’a S.P Gang ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranakun uku da hudu ga watan Maris masu zuwa.