Wani dalibin ajin karshe a Jami’ar Tarayya ta Kashere da ke Jihar Gombe, Nalkur Zwalnan Lar ya kashe kansa saboda ya gaza mallakar wayar salula ta naira dubu hamsin.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, Nalkur ya kashe kansa ne a unguwar Santuraki da ke garin Kashere a daren ranar Laraba.
- 2023: Kotu ta kori dan takarar gwamnan APC a Ribas
- A duba cancanta wajen zaben shugabanni a 2023 —Isaac Idahosa
Majiyar rahoton ta ce dalibin wanda ke karatu a Tsangayar Nazarin Koyarwa ya kashe kansa ne bayan ya sha guba, kuma bayan hakarsa ba ta cimma ruwa ba ya rataye kansa a jikin wata itaciya.
Cikin wani sako da ya rubuta da hannunsa kafin wannan danyen aiki, dalibin ya yi wa yayyansa maza godiya wanda ya ce sun yi masa komai a rayuwa.
Haka kuma, dalibin ya bukaci mahaifiyarsa wadda ya bayyana a matsayin mafificiyar uwa a duniya da ta dauki dangana.
A cikin wasikar, dalibin ya bayyana cewa bai san dadin rayuwa ba, yana mai ikirarin cewa mahaifinsa ya mallaki miliyoyin naira amma shi kuwa ko wayar naira dubu hamsin ta gagare shi.
Marigayin ya kuma zayyana sunayen mutanen da suke binsa bashi da kuma yadda za su samu kudinsu.
Kazalika, ya nema gafarar wasu mutum biyu da ya bayyana sunayensu –Favour da Comfort.
Da aka tuntubi Shugaban Sashen Tsare-Tsare da Bayanai na Jam’iar Kashere, Suleyman Malami Ahmed, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce za su fitar da jawabi a nan gaba da zarar sun kammala bincike.