✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalibi ya kashe kansa bayan an cinye kudin makarantarsa a cacar intanet

ya yi wannan aika-aika ne a yayin da ake shirin fara jarabawar kanshen zangon karatu.

Wani dalibin Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Tarayya da ke Ilaro, ya kashe kansa, bayan da ya buga cacar intanet da kudin makarantarsa, aka kuma cinye shi.

Aminiya ta gano cewa bayan dalibin ya yi cacar intanet da kudin makarantarsa aka cinye shi, sai ya yi afamni da kudin wani abokin karatunsa ya sake bugawa, nan ma aka cinye shi.

Ana zargin dalibin, wanda yake shekara ta biyu a matakin Difloma, ya kwankwadi guba ne saboda takaicin cinye kudaden da aka yi a cacar (wadda aka fi sani da betting) da ya buga ranar Juma’a.

Shaidu sun ce dalibin, wanda ke karatu a fannin Injiniyan Lantarki, ya yi wannan aika-aika ne a ranar Litinin a yayin da ake shirin fara jarabawar kanshen zangon karatu.

An garzaya da shi zuwa asibitin makarantar, amma bin ya gagara, sai da aka kai shi Asibitin Kwararru na Ilaro, inda a nan likitoci suka sanar cewa rai ya yi halinsa.

Mai magana da yawun Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Tarayya da ke Ilaro, Sola Abiala, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Matsalar cacar intanet tsakanin matasa, musamman masu bibiyar harkar kwallon kafa dai na neman zama karfen kafa, inda a wasu lokutan wasu ke cin bashi ko kuruciyar bera domin samun kudin bugawa.

Masana da dama dai sun danganta hakan da yadda matasa suke neman yin kudi ido rufe, wanda hakan ke cikin abubuwan da ke wasunsu shiga harkar damfara ta intanet, wanda aka fi sani da Yahoo.