✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɗalibi ya kashe abokin karatunsu da gatari a Nasarawa

Ya yi amfani da wuƙa da kuma gatari wajen halaka abokin nasa a gidan da suke haya bayan wata hatsaniya a tsakaninsu.

Wani ɗalibi a Kwalejin Kimiyya da Ƙere-kere ta Tarayya da ke Jihar Nasarawa ya yi wa abokin karatunsa kisan gilla ta hanyar amfani da wuƙa da gatari.

Rundunar ’Yan Sanda Jihar Nasarawa ta ce ɗalibin da ya yi kisan gillar ɗan ajin ND2 a Fannin Aikin Banki da Hadahadar Kuɗaɗe ne a Kwalejin kuma yana hannunta, yana amsa tambayoyi.

Ta bayyana cewa ya amsa laifin tare da shaida wa masu bincike cewa ya yi amfani da wuƙa da kuma gatari wajen halaka abokin nasa a gidan da suke haya bayan wata hatsaniya a tsakaninsu.

Kakakin rundunar, Rahman Nansel, ya bayyana cewa jami’an rundunar sun kai ɗauki ne bayan matar da ɗaliban ke haya a gidanta, Mercy-Bassey, ta sanar da rundunar cewa rikici ya ɓarke a tsakanin maƙwabtakan nata.

Ya ce ko da jami’an suka isa, sai suka tarar da gawar ɗaya ɗalibin ɗan abin ND2 a Fannin Kimiyyar Kwamfuta kwance a cikin jini a cikin ɗakin.

Jami’in ya ce an garzaya da shi Babban Asibitin Nasarawa, inda likitoci suka sanar cewa rai ya riga ya yi halinsa saboda tsananin raunukan da ya samu.

Ya ce Kwamishinan ’yan sandan jihar, Shettima Jauro-Mohammed ya ba da umarnin a tsananta bincike a kan lamarin.

Tuni aka ɗauke makaman da sauran abubuwan da aka iske a wurin da abin ya faru a matsayin shaida, gawar kuma an kai ta ɗakin ajiyar gawa domin gudanar da bincike.