✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalibi ya harbe mutum 19 a makarantarsu a Amurka

Dalibin ya harbe kakarsa kafin ya je makaranta ya hallaka mutum 19

Dalibai firamare akalla 12 sun rasu tare da malaminsu da wani dan sanda bayan wani dalibi ya bude wuta wata makarantar firamare da ke Jihar Texas na kasar Amurka.

Shaidu sun ce yawancin daliban da dalibin mai shekara 18 ya kashe ’yan aji uku da aji hudu ne, sai kuma wani malami a harin na Makarantar Robb Elementary da ke yankin Uvalde.

Gwamnan Jihar Texas, Greg Abbott, ya ce, wanda ake zargin, dalibin makarantar ce, kuma “ya harbe sama da mutum 20 a wani yanayi ma ban tsoro da hankali ba zai dauka ba.”

Akalla wasu daliban makarantar 15 da dattawa uku ne aka kwantar a asibitoci sakamakon raunukan da suka samu a sanadiyyar harin.

Ana kuma zargin sai da dalibin wanda ba a bayyana sunansa, Salvador Ramos, ya harbe kakarsa a wani wuri daban, kafin ya shiga harabar makarantar ya bude wuta.

Jami’an tsaro sun ce sun yi musayar wauta da dalibin, kafin daga baya ya shiga motarsa ya yi karo da ita, wanda hakan ya yi sanadaiyyar mutuwarsa.

Wasu mutane suna lallashin wata daliba a Uvalde, Texas, ranar Talata, 24 ga Mayu, 2022, bayan harin da dalibin ya kai a makarantar. (Hoto: Allison Dinner/AFP)
Wasu mutane suna lallashin wata daliba a Uvalde, Texas, ranar Talata, 24 ga Mayu, 2022, bayan harin da dalibin ya kai a makarantar. (Hoto: Allison Dinner/AFP).

Sun ce an gano bindiga kirar AR-15 da kwansaon harsadasi da dama a hannun matashin, a cewar kafar yada labarai ta ABC News.

Jami’an tsaron kan iyaka na Amurka sun kai dauki bayan samu kiran gaggawa daga jami’n tsaron makarantar, inda da suka kai dauki tare da yin musayar wuta da dalibin.

’Yan sanda biyu na daga cikin wadanda suka jikkata a cewar gwamnan jihar, amma ya ce ana kyautata zaton za su mike.

Akwai kima jami’in tsaron iyaka da ya samu raunuk a yayin da yake kokarin kare dalibai daga harin dan bindigar.

Matsalar harin bindiga musamman a makrantau da wurarn taron jama’a sun kazanta a Amurka, inda a lokuta da dama ake kashe fararen hula, sai kuma maharan, da a wasu lokuta suke kashe kansu.