✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Daliban Kankara sun sauka a Gidan Gwamnatin Katsina

Daliban Kankara da ’yan bindiga suka sako sun isa Katsina

Da safiyar Juma’a daliban Makarantar Kankara 344 suka sauka a Jihar Katsina bayan ’yan bindiga sun sake su a Jihar Zamfara.

Daliban su 344 sun sauka ne a Gidan Gwamnatin Jihar Katsina inda suka samu tarba daga jami’an gwamnati.

An ga daliban, wasunsu sanye da kayan makaranta sun yi dogon layi suna ta shiga cikin ginin Gidan Gwamnatin, bayan sun sauka daga motocinda suka ajiye su a cikin a harabar Gidan Gwamnatin.

Daliban sun samu rakiyar jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.

Ranar Alhamis da dare ne dai ‘yan bindiga suka sako daliban su 344 da suka yi garkuwa da su bayan an tattauna da su da wakilan gwamnati.

Karin Labarinna tafe…