Kwana daya da ceto wasu dalibai biyar na Kwalejin Gandun Daji da ke Afaka, Jihar Kaduna, har yanzu iyayensu sun ce ba su yi tozali da su ba.
Aminiya ta rawaito a ranar Litinin cewar sojoji sun kubutar da dalibai biyar daga cikin 39 da aka yi garkuwa da su a ranar 11 ga watan Maris, 2021 daga kwalejin.
- A shirye muke a kashe mu kan ceto ’ya’yanmu —Iyayen dalibai ga El-Rufai
- Buhari ya nada sabon Shugaban ’Yan sandan Najeriya
- Watan Azumi: Za a rage farashin kayan abinci da kashi 75
- ’Yan bindiga sun harbe Hausawa bakwai a Jihar Imo
Daya daga iyayen daliban, Friday Sanni, ya ce “Ba mu san su wa aka saki daga cikin daliban ba, mun je don mu gana da su an ce mana sai an kammala bincike sannan za a ba mu damar ganawa da su”.
Sai dai Gwamnatin Jihar Kaduna ba ta bayyana yadda aka kubutar daliban ba, amma ta ce an kai su sansanin soji, inda ake kula da lafiyarsu.
Dalibai biyar din da aka kubutar sun shafe tsawon kwana 25 a hannun wanda suka yi garkuwa da su, kafin su samu nasarar shakar iskar ’yanci.