Dalibai takwas da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su daga Jami’ar Tarayya ta Lafia da ke Jihar Nasarawa sun kubuta.
A ranar 6 ga wata ne ’yan bindiga suka kutsa unguwar Gandu da ke Lafia suka yi awon gaba da daliban, daga dakunan kwanansu a unguwar.
Wani shugaban al’umma a yankin Keana, Spencer Jerry, ya ce ɗaliban sun iso yankin Kwarra a ranar Lahadi da dare, daga nan aka kai su wurin jami’an tsaro.
Hakimin Gandu, Abdullahi Mohammed ya ce an kai ɗaliban asibitin da ke cikin jami’ar domin duba lafiyarsu.
- ’Yan Arewa a Majalisar Tarayya sun ba da gudummawar N45m
- Fitacciyar mai karanta labaran NTA, Aisha Bello ta rasu
Amma jami’ar, Abubakar Ibrahim, ya tabbatar cewa an sako su da misalin karfe 8 na ranar Lahadi, kuma ana duba lafiyarsu.
Jami’in ya ce hukumar jami’ar da gwamnatin jihar sun hada kai wajen tsaurara matakan tsaro domin hana aukuwar irin haka a nan gaba.
Ya kuma bukaci gwamnatin jihar ta yi cikakken bincike domin gano ainihin abin da ya fari
Wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sandan jihar Nasarawa DSP Rahman Nansel domin samun karin haske a kan lamarin.
Amma jami’in ya shaida masa cewa rundunar ba ta da labarin sace daliban ko na sakin su a hukumance.