✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Daliban da aka sace daga makarantar Kaduna sun haura 100

Wani ma’aikacin makarantar ya ce daliban da aka sace za su iya kaiwa 140.

Wasu daga cikin iyayen daliban da aka sace daga makarantar Bethel Baptist da ke garin Kujama a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna sun ce yawan ’ya’yan nasu da aka sace sun haura 100.

Da sanyin safiyar Litinin ne dai wasu ’yan bindiga dauke da muggan makamai suka fasa ginin makarantar sannan suka sace dalibai da dama a daga cikinta.

Da wakilin Aminiya ya ziyarci makarantar da safiyar ranar Litinin, ya iske wasu daga cikin iyayen yaran suna tattauna batun.

Wani ma’aikacin makarantar da bai amince a ambaci sunansa ba saboda bashi da hurumin yin magana ya ce dalibai 140 ne aka sace.

“Sama da dalibai 140 ne aka sace da suka hada da maza da mata, ko da yake har yanzu makaranatar na ta kokarin tattara sunayensu, amma akwai yuwuwar alkaluman ma su zarce hakan,” inji shi.

A wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya fitar ranar Litinin, ya ce jim kadan da samun rahoton satar daliban, jami’an tsaro suka bazama don ceto su.

Ya ce tuni rundunar wacce ta kunshi gamayyar ’yan sanda da sojojin kasa da na ruwa suka sami nasarar ceto dalibai 26 da kuma wata malama guda daya daga hannunsu.