✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalibai sun kashe matashiya a Sakkwato saboda zargin batanci ga Annabi

Ana zarginta ne da yin batancin a dandalin WhatsApp na ajinsu

Dalibai a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato Sun kashe abokiyar karatunsu bayan sun zarge ta da zagin Annabi Muhammad (S.A.W.).

Ana zargin dalibar mai suna Deborah ce da yin batancin a dandalin sada zumunta na WhatsApp.

Dalibar ta yi zagin ne kan hassalata da ’yan uwanta suka yi na tura abubuwan da suka shafi Manzon Allah a group na karatunsu wanda take ganin hakan bai dace ba.

Matasan sun fusata suka nemo ta a cikin makaranta suka kashe ta anan take kuma suka kona gawarta.

Daga bisani dai hukumar makarantar ta bayar da sanarwa rufe kwalejin har sai abin da hali ya yi, tare da umartar dalibai su bar makarantar nan take.

Jami’in huda da jama’a na kwalejin, Kabiru Yabo, ya ce za su yi magana kan lamarin daga baya.

Duk kokarin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin ’yan sandan Jihar ta Sakkwato, Sanusi Abubakar, ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoton.