Akalla dalibai 30 ne suka kamu bayan barkewar wata bakuwar cuta a Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamanti da ke Sakkwato.
Darektan Lafiya a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Sakkwato, Abdurrahaman Dantsoho, ya ce an fara gudanar da bincike a kan kayan abinci da sauran abubuwan domin gano musabbabin barkewar cutar.
- Yadda kayan hada rabobi ka sa kankancewar al’aura —Bincike
- Badala: Hisbah ta kama daliban jami’a suna sheke ayarsu a Kano
- An kama matar da ta kashe kishiyarta ta kona gawar
- Yadda gasar karatun Al-Kur’ani ta Kasa ke gudana a Kano
Kwamishinar Ilimi da Kimiya da Kere-Kere ta Jihar, Kulu Haruna, ta ce “An killace daukacin daliban da suka kamu domin hana yaduwar cutar ga wasu.
“An yi nasarar shawo kan lamarin sakamakon matakan gaggawa da Gwamnatin Jihar ta dauka,” inji ta tana mai cewa an tura likitoci 10 zuwa asibitin domin kula da daliban.
A nasa bangaren, Danstoho ya tabbatar cewa an sallami duk daliban bayan barkewar cutar a ranar Talata, wadda kuma ta yi sanadiyyar kwantar ta su a wani asibitin kwararru.
Ya kuma karyata jita-jitar da ya ce ana bazawa cewa cutar ta yi ajalin wasu daga cikin ’yan matan sakamakon cutar da ba kai ga ganowa ba.