Wani bincike da jaridar Aminiya ta gudanar ya gano cewa jami’o’i da manyan kwalejojin kasar nan dalibai kashi 26 kawai za su iya baiwa guraben karatu saboda karancin guraben da suke da shi.
Alkalman da hukuma ta fitar sun nuna fiye da dalibai miliyan 10 ne suka nemi shiga jami’o’i a cikin shekaru shida wato da shekarar 2010 zuwa shekarar 2015 amma dalibai miliyan biyu da dubu 674 da 485 kawai suka sami guraben karatu.
Wannan adadi kamar yadda Hukumar Kididdiga ta NBS da kuma shafin yanar gizo na hukumar JAMB ta kasa suka nuna ya kai adadin daliban da suka zauna jarabwar neman shiga jami’a ta UTME a duk shekara.
Kimanin kashI 74 cikin dari na wadanda ba su sami gurbin karatu ba an tilasta musu su jira zuwa shekara mai zuwa don sake neman gurbin karatun tare da daliban da suka kammala sakandire a shekarar.