Wasu dalibai biyar daga cikin 39 da aka yi garkuwa da su a Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke Jihar Kaduna sun kubuta.
Rundunar sojin Najeriya ce ta sanar da Gwamnatin Jihar batun gano daliban da aka sace tun a watan jiya.
- Bishop Kukah ya caccaki Buhari kan matsalar tsaro
- Masoyan Buhari sun mamaye gidan Gwamnatin Najeriya a Landan
- A shirye muke a kashe mu kan ceto ’ya’yanmu —Iyayen dalibai ga El-Rufai
Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Jihar Kaduna ta wallafa a shafinta na Twitter da yammacin ranar Litinin cewa daliban na hannun jami’an tsaro domin tabbatar da koshin lafiyarsu.
Ta kara da cewa, da zarar an samu wani karin bayani kan halin da ake ciki za ta fidda wata sanarwar ta daban domin karin haske.
A cikin watan Maris din da ya gabata ne aka sace dalibai a kwalejin da ke Afaka.
A lokacin da maharan suka kai farmaki da tsakar dare, an yi dauki ba dadi tsakaninsu da jami’an tsaro da suka yi nasarar kubutar da mutum 180 daga kwalejin.
Sanarwar da rundunar sojin ta fitar a wancan lokaci, ta ce an samu ceto mutane 100 da suka hadar da dalibai mata 42 da dalibai maza 130 da kuma da malamai takwas.
Saura dalibai 25 a hannun ’yan bindiga
Ya zuwa yanzu, akwai sauran dalibai 25 da har yanzu suna hannun maharan da suka sace su tsawon makonni hudu da suka shude.
Masu garkuwa da su na bukatar kudin fansa Naira miliyan 500 amma Gwamnatin Jihar ta ce ko sisi ba za ta biya ba, kuma ba za ta tattauna da ’yan bindigar domin su sako su ba.
Gwamna Nasir El-Rufai ya yi barazanar hukunta duk wanda ta samu yana tattauanawa da masu garkuwa da mutane.
Gwamnati ta gaza, Ba mai hana mu tattaunawa
amma iyayen daliban sun ce su za su tattauna da su domin ceto rayukan ’ya’yan nasu.
Sun ce tun da bayan mako hudu gwamnatin “ta kasa yin wani abin a zo, a gani don kubutar da daliban,” su a matsayinsu na iyaye, za su yi duk abin da za su iya, matukar ’ya’yansu za su tsira, ko da kuwa za a kashe su ko a tsare su ne.
Sakataren kungiyar iyayen daliban, Sanni Friday, ya ce matukar za a sako musu ’ya’yansu, to a shirye suke su sayar da yarukanmu ko a tsare su.
Ya bayyana cewa za su tattauna ne da masu garkuwar a matsayinsu na iyayen daliban domin su ceto rayuwar ’ya’yansu, ba da yawun gwamnati ba.
“Muna fada da babbar murya cewa a matsayinmu na iyaye, ba za mu nade hannu mu ki yin komai ba, za mu yi duk abin da za mu iya yi domin kubutar da ’yan’yanmu cikin koshin lafiya.
“Muna jaddada cewa, da yardar Allah, za mu yi duk abin da ba zai gagare mu ba, na ganin ’ya’yanmu ba su halaka ba”, inji kakakinsu, Samuel Kambaia ranar Litinin.