Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’o’i a Najeriya (JAMB) ta ce an samu masu rubuta jarrabawar kimanin 60,000 da suka gamu da cikas a cikin kwana biyun da suka wuce.
Wannan adadin dai wani kaso ne a cikin mutum 947,000 da suka rubuta jarrabawar JAMB a wannan lokaci.
Shugaba sashen hulda da jama’a na hukumar, Dokta Fabian Benjamin ne ya bayyana haka bayan rangadin wuraren da ake rubuta jarrabawar tare da Babban Magatakardan hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede da sauran jami’ai ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce an sake sanya daliban lokacin da su je su rubuta jarrabawar tasu.
Ya ba da tabbacin cewa za a bai wa duk wanda ya yi rijista don rubuta jarrabawar JAMB dama yin hakan, yana cewa hukumar ta shawo kan matsalolin na’urorin da aka fuskanta a ranar farko ta rubuta jarrabawar a wasu cibiyoyi da ke faɗin ƙasar.
Dokta Fabian Benjamin ya ce wannan ce jarrabawa mafi inganci da suka taba yi a tsawon shekaru, ko da yake ya san wasu za su yi jayayya da abin da ya fada saboda matsalolin da aka samu ranar Talata.