Kimanin sa’a 48 bayan harin ’yan bindiga a Makarantar Sakandaren Kimiyya da ke Kankara (GSSS Kankara), Jihar Katsina, har yanzu ba a san inda dalibai 333 suke ba.
Gwamnan Jihar, Aminu Bello Masari wanda ya rufe makarantun kwanan jihar bayan harin ya bayyana haka ne a ranar Asabar, ranar da iyayen dalibai suka yi zanga-zanga da addu’o’i domin kubutar da ’yan makarantar.
“Bayanin da muke da shi zuwa yanzu shi ne, dalibai 333 ne ake nema a cikin dazuka ake kuma tuntubar iyaye domin a gano ainihin adadin wadanda aka yi garkuwa da su”, inji Gwamna Masari.
Ya sanar da hakan ne yayin da Ministan Tsaro, Bashir Magashi da Manyan Hafsoshin Tsaro da sauran shugabannin hukumomin tsaro suka kai masa ziyarar jaje kan harin ’yan bindigar.
Kawo yanzu dai ba a kai ga tantance adadin daliban da ’yan bindigar suka sace a harin na ranar Juma’a, ’yan sa’o’i bayan Shugaba Buhari ya fara ziyarar mako guda a jihar.
Masari ya bayyana wa tawagar cewa: “Yaran da aka yi garkuwa da su sun fito ne daga fadin jihar, domin makarantar kwanar ta tattaro dalibai ne daga sassan jihar da ma wasu jihohin.
“Daibai 839 ne a makarantar amma har yanzu ba mu san inda 333 suke ba; Muna ci gaba da kirga saboda wasunsu na kara fitowa daga cikin daji, muna kuma tuntubar iyayen da muke da lambobinsu mu ji ko yaran sun koma gida ne”.
Ya ce har yanzu ’yan bindigar ba su tuntubi gwamnatin jihar ko wani ba game da daliban da aka yi garkuwa da su.
Gwamnan wanda ya bukaci a iyaye da su yi hakuri za a gano yaran, ya kuma yi kira ga iyayen da ’ya’yansu suka koma gida da su sanar da hukumar makarantar.
A nashi bangaren, Ministan tsaro, Bashir Magashi ya ce na da ’yan sa’o’i masu zuwa za a kwato daliban cikin koshin lafiya ba tare da wata asara ba ga jihar.
Magashi ya ce tuni hukumomin tsaro suka fara aiki, kuma sun riga sun tsara yadda aikin ce daliban zai kasance ta hanyar amfani da bayanan sirrin da suka riga suka tattara.
Ministan tsaron, wanda ya la’anci harin, ya ce lokaci ya yi na Gwamnatin Tarayya ta ayyana ayyana masu garkuwa da mutane a matsayin ’yan ta’adda domin hakan zai sa a tashi tsaye wurin yakar su.