✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalibai 179 sun kammala Digiri da Daraja ta Ɗaya a Jami’ar Bayero

Dalibai 179 za su samu shaidar Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a yayin bikin yaye dalibai Jami'ar Bayero ta Kano (BUK).

Dalibai 179 za su samu shaidar Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a yayin bikin yaye ɗalibai na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK).

Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Abba, ya bayyana cewa dalibai 4,402 ne za a yi bikin yaye su a ranar farkon, inda a za a ba su shaidar kammala Digirin farko da Difloma da sauran makamantansu.

Bikin yaye ɗaliban shi ne karo na 39 da za a gudanar a jami’ar ta BUK.

Bikin na kwana huɗu ya kunshi jawabai da laccoci da taruka da kuma bayar da kyaututtuka da takardun shaida a matakai daban-daban.

Farfesa Sagir Abbas ya bayyana cewa a rana ta biyu za a yaye ɗalibai 4,367 daga tsangayu bakwai.

Daga cikinsu mutum 275 za su samu shaidar Digiri na Uku (PhD), 2,590 kuma masu Digiri na Biyu, sai musu 535 masu Diflomar Gaba da Digiri (PGD).

Akwai kuma waɗanda za a ba wa Digirin Girmamawa (Honoris Causa) da kuma Farfesan Ferfesoshi (Emiritus).