Ana zargin wata dalibar aji hudu a Jami’ar Olabisi Onabanjo (OOU) da ke Jihar Ogun ta kashe kanta ta hanyar shan guba a wani dakin dakin otel.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ta ce an gano dalibar, Adaze Doris Jaja, mai shekaru 31 ne a sume a cikin dakin, kumfa na fitowa daga bakinta, da kwalbar maganin kashe kwari a gefenta.
Odutola ta shaida wa ’yan jarida a Abeokuta ranar Talata cewa ranar 27 ga watan Janairu da karfe 7:30 na safe, an kai rahoton lamarin ga jami’in ’yan sanda na Ago-Iwoye, yankin da abin ya faru.
Odutola ta “Daraktan otal din Be-Happy da ke Ago-Iwoye, Oduniyi Adelaja, ya kai rahoto ofishin ’yan sanda cewa da misalin karfe 6 na safiyar ranar, ya samu labari daga wani ma’aikacin otal din cewa an iske Adaeze a sume a dakinta kumfa na fitowa daga bakinta, da wata kwalbar maganin kashe kwari a gefenta.
- Hanyoyin Da ‘Yan Arewa Za Su Ci Moriyar Soshiyal Midiya
- Ta bar wa kare da kyanwa duk N2bn ta hana ‘ya’yanta
“Nan take aka garzaya da ita asibiti inda daga bisani aka tabbatar da mutuwarta,” in ji jami’ar.
Odutola ta ce an ziyarci inda lamarin ya faru kuma an gano fankon robar maganin kashe kwarin.
Ta kuma bayyana cewa an kai gawar dalibar zuwa dakin ajiye gawa na asibitin koyarwa na OOU domin bincike.
Jami’ar ta kara da cewa rundunar ta fara gudanar da bincike kuma ta sanar da hukumomin jami’ar game da lamarin.