✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta cinye dakunan kwanan dalibai 16 a Kano

Gobara ta cinye dakunan kwanan dalibai a Kwalejin Koyar Aikin Jinya da ke Kano.

Kimanin dakunan kwanan dalibai 16 ne suka kone sakamakon tashin gobara a Kwalejin Koyar Aikin Jinya da Ungozoma da ke Kano.

Gobarar ta tashi ne bayan idar da sallar Magriba da maraicen Laraba, ta kuma kwashe kimanin sa’a biyu tana ci kafin jami’an kashe gobara su shawo kanta.

Wata daliba da ta shaida faruwar lamarin ta bayyana cewa gobarar ta cinye akalla dakuna 16 a hawa na uku da ke rukunin dakunan kwanan dalibai na Sa’idu Fagge da ke kwalejin.

“Dakuna 16 ne suka kone, tukwanen gas haka suka dinga fashewa.

“Ko tsinke ba mu dauka ba, duka kayayyakinmu sun kone kurmus.

“’Yan kwana-kwana ba su zo da wuri ba sai da gobarar ta ci iya cinta.

“Yanzu daliban da ba ’yan Kano ba suna nan cikin tashin hankali ba su ma san ina za su sa kansu ba”, a cewarta.

Zuwa yanzu dai ba a tabbatar da musabbabin tashin gobarar ba a hukumance.