Daya daga cikin Limaman masallacin gidajen ’yan majalisa da ke Apo a Abuja, Imam Ibrahim Awwal, ya ce dakatarwar da aka yi wa Babban Limamin Masallacin, Sheikh Nuru Khalid ba zai sa su daina fadin gaskiya ba.
Imam Ibrahim, wanda aka fi sani da Usama, ya bayyana haka ne a yayin zantawarsa da wakilin Aminiya a Abuja ranar Litinin.
- Gwamnati ta ba da umarnin toshe duk layukan wayar da ba a hada da NIN ba
- ’Yan bindiga sun kashe dan Kwamishinan Tsaron Zamfara
Ya ce a baya babu abin da basu faba ba kan gwamnatin tsofaffin Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.
Ya ce babu irin lallashinsu da ba ayi ba, na su bar abin da suke fada, amma suka ki bari, saboda ya ce gaskiya suke fada.
Imam Usama ya kuma ce, “In dai don abin da ya fada ne na cewa gwamnati ta gyara kura-kurenta, aka dakatar da shi, to akwai kuskure.
“Amma idan ya ce ’yan Arewa kada su fito su yi zabe ne saboda matsalar tsaron da ke faruwa, ba a yi daidai ba. Domin fadakarwa ya kamata a yi wa mutane su fito su zabi shugabanni na gari.
“Kuma wannan abu da aka yi, ba zai sa mu yi shiru da fada wa gwamnati gaskiya ba, matukar ta yi abin da bai dace ba. Domin Allah ne ya ce mu yi haka,” inji Limamin.
Ya ce bai kamata malamai su yi shiru kan abin da ya shafi fadin gaskiya ba, matukar suka ga gwamnati tana neman sakin layi.
Imam Ibrahim ya bayyana abin da ya faru da Sheikh Nura Khalid a matsayin nasara ga malamai, don su kara tsayawa kan gaskiya.