Tsohon dan Majalisar Tarayya kuma dan Takarar Gwamna a Jahar Adamawa, Cif Emmanuel Bello ya mayar da martani ga ‘yan jam’iyyar tasa karkashin jagorancin Dakta John Luka wadda suka shirya taro domin dakatar da shi daga yin takara, inda a cewarsa dakatarwar ta boge ce, sannan hakan ba zai razana shi ba.
Ya ce wannan dakatarwar da suka yi ba wani abu ba ne illa hassada da bakin ciki da suka yi masa, kuma nan ba da dadewa ba za su sha kunya. Ya kara da cewa wannan aibanta shi da Dokta Luka ya yi ba girmansa ba ne, kuma bai kamanci kowane mamba na jam’iyyar SDP a lokacin da ake cikin kafa sabon kwamiti a dakatar da wani daga zabe ba.
“Idan ba za ku manta ba, Dakta John Luka Njiling a wani taro da ya kira na manema labarai, ya yi kazafi da dama wadanda ya ce ni ba cikakken mamban Jam’iyyar SDP ba ne, sannan ina shirin hada wata kungiya da manufarta ta sha bamabam da na SDP da dai sauransu,” in ji shi.
“Wannan kazafi ba wani abu ba ne illa sharri da bata min suna, don haka ina kiran al’umma da su guji daukar wannan magana ta Luka, domin ya yi ne da nufin bata mini suna,” a cewarsa.
Mataimakin Emmanuel Mustapha ya ce akwai Manjo Janar John Zaruwa wadda aka aikowa jam’iyyar SDP ta Yola, domin daidaita kansu a jahar kuma Luka ya yi wannan kazafin a washe garin zuwan Manjo Janar Zaruwa ne, a cewarsu hakan bai dace ba daga tsarin gudanar da harkokin jam’iyyar. Emmanuel Bello dai kwanan nan ya canza sheka daga APC zuwa SDP, inda ya bayyana manufarsa ta tsayawa takarar gwamnan jahar a shekarar 2019.