Dakataccen Shugaban PDP a Jihar Ondo, Fatai Adams ya rasu, kwanaki 43 bayan dakatar da shi daga jam’iyyar.
Fatai Adams, ya rasune sakamakon ciwon kai a gidansa da ke Ikare Akoko a daren Talata.
Kwamitin Gudanarwan PDP na jihar sun dakatar da Adams ne a ranar 2 ga Janairu, 2024 saboda zargin zagon gaka ga jam’iyyar.
An kuma zarge shi da yin wasu abubuwa da ka iya janyo wa jam’iyyar adawar abin kunya.
- Yadda Aka Kama Sojan Da Ke Kai Wa Bello Turji Kayan Yaki
- An daure Maman Boko Haram shekara 10 a kurkuku
Dakatarwar ce ta ba da damar zaman Mista Tola Alabere shugaban riko.
Mun kasa samun kakakin jam’iyyar PDP na jihar, Kennedy Peretie domin jin ta bakinsa kan lamarin.