Daya daga cikin Daraktocin Kamfanin Media Trust masu wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya da sauransu, Alhaji Rabi’u Garba, ya rasu a Yammacin ranar Talata bayan shafe shekaru 63 a doron kasa.
Dangin mamacin sun bayyana cewa ya shafe fiye da tsawon wata guda yana jinya a wani asibitin a Kasar Masar, inda dan uwansa, Saminu Garba ya tabbatar da cewa a halin yanzu ana shirin dawo da gawarsa gida Najeriya.
- Gwamnan Benuwai ya kamu da Coronavirus
- Mai Garin da aka sace a Katsina ya kubuta
- Bakuwar cuta ta kashe mutum 4 a Sakkwato, 24 sun kwanta a asibiti
Kafin rasuwarsa, Alhaji Rabi’u shi ne Shugaban Kamfanin wallafa da tallace-tallace na ESPEE da ke Jihar Kaduna.
Alkaluma na tarihi sun nuna cewa an haifi Alhaji Rabi’u a ranar 21 ga watan Yunin 1957, kuma ya kasance Shugaban Kwamitin Wallafa da Buga Jaridu na Kamfanin Media Trust har zuwa bara inda ya karbi jagorancin Kwamitin Tuntuba da Kula da Harkokin Kasuwanci na Kamfanin.
Alhaji Rabi’u wanda shekaru uku da suka gabata yayin bikin cikar Kamfanin Media Trust shekaru 20 da kafuwa, ya zayyana yadda Jaridar Daily Trust wacce a baya ake kira Weekly Trust ta fara a wani dan karamin gini wanda ya misalta kankantarsa da dakin saukar baki a gidansa.
Shugaban Kamfanin, Malam Kabiru Yusuf, ya bayyana cewa gudunmuwar da Marigayi Alhaji Rabi’u ya bai wa Kamfanin wajen samun nasarori ba za ta misaltu ba.
Malam Kabiru ya ce Marigayi Garba kafin mutuwarsa, ya kasance daya daga cikin masu hannayen jari kuma Darakta a Kamfanin Media Trust tun fil azal.
Marigayi Alhaji Rabi’u ya rasu ya bar mata daya, ’ya’ya biyar da jikoki uku, kuma mafi shahara a cikin ’ya’yansa shi ne Umar Rabi’u Garba, wanda ma’aikaci ne a Kamfanin wallafa da tallace-tallace na ESPEE da ke Jihar Kaduna.