Tun bayan da aka janye dokar zaman gida a ranar Litinin din makon jiya a jihohin Legas da Ogun da kuma Yankin Babban Birnin Tarayya, mazauna wadannan yankuna suke bayyana ra’ayoyi daban-daban game da lamarin.
Zaman kullen da aka shafe wata guda cur ana yi ya rufe duk wasu ayyuka in ban da wadanda suka zama lallai da tilas.
Duk da samun sabbin masu kamuwa da cutar coronavirus a Najeriya, a ganin wasu sassauta dokar wani ‘yanci’ ne yayin da wasu kuma ke ganin hakan a zaman wani ‘mataki da zai kara munana lamarin’.
- Buhari ya amince da sassauta doka sannu a hankali
- Buhari ya ba da umarnin hana fita a Abuja da Legas
Aminiya ta tattauna da wasu mazauna Abuja game da sassauta zaman kullen da kuma don jin matakan da suke dauka domin kare kansu.
”Yanci ya samu’
“Ah! Yanci ya samu daga karshe! Ina matukar farin ciki, duk da cewa ma tun farko ban yarda akwai wannan cutar ba.
“Gwamnati ta kulle mu ne kawai a cikin gida”, inji Dennis Theophilus, wani dan tasi, wanda ke cike da murnar komewa bakin aikinsa bayan zaman kullen.
“Karuwar masu kamuwa da cutar abin damuwa ne sosai, za a fahimci haka ne karshen dokar kullen.
“Wadanda suke dauke da cutar sun zauna a gida bayan sun yi gwajin da ya tabbatar da suna dauke da ciwon.
“Amma da yake yanzu an sassauta zaman kullen, akwai yiwuwar yawan masu kamuwa da cutar ya yi tashin gwauron zabi – saboda mutanen da suka kasance suna kare kansu yanzu za su cakuda da masu dauke da ciwon,” a cewar wani ma’aikaci mai suna Musa Kabiru.
Abin da zai faru
Lokacin da wakilan Aminiya suka yi kicibis da wata mai suna Nkiru Nnamdi a cikin rumfarta da ke kasuwar Karmo a nan Abuja, tana mai yin nesa-nesa ta bayyana cewa, “Ina ta tunanin abin da zai faru nan da kwana 21 masu zuwa – yayin da za a shaida sakamakon da sassauta dokar zai haifar.
“Mutanen da ba su san matsayarsu game da cutar ba za su rika mu’amala da sauran jama’a a wajen shiga mota da kuma mu’amalar canjin kudi — wadannan abubuwan kawai za su haifar da yada cutar”, Inji ta.
“Zama cikin kare kai a yanzu da aka sassauta zaman kullen zai zama tamkar rakumi ya wuce ta cikin kofar allura ne. Duk da kasancewar ni ina yawo ne, har yanzu ina shakku kan wasu abubuwa kamar taba kyauren motata, saboda ba zan iya sanin wanda ya taba motar a lokacin da na ajiye ta ba,” a cewar wata mai suna Rukayat Ajayi.
Aminiya ta lura cewa, wasu mazauna Yankin Babban Birnin Tarayyar ba su damu da bayar da tazara ga juna tare da daukar sauran matakan kariya a wurare ba.
Don haka, wane ne zai yi hasashen abin da zai biyo bayan sassauta dokar zaman kullen da gwamnatin ta yi?
Ranar 30 ga watan Maris din 2020 ne dai gwamnatin tarayya ta yi shelar kafa dokar zaman gida a Abuja da jihohin Legas da kuma Ogun.