Wata mara lafiya da ta tare a coci domin neman lafiya na zargin limamin cocin da yi wa ’ya’yanta biyu fyade.
Matar ta ce faston ya lalata ’ya’yan ta biyu masu shekaru 16 da 13 har suka yi ciki bayan ta tare a cocinsa da ke olumore a Abeokuta a shekara 2018 a kokarinta na neman maganin cutar da ke damunta.
Ta ce bayan an kai ta cocin sai ya bukaci ta tare a cocin tare da ’ya’yanta su shida domin gudun kada cutar ta shafi yaran, amma ya yi amfani da damar ya yi ta lalata da yaran har ya masu ciki.
Ta kara da cewa bayan ya tabbatar sun dauki ciki sai ya kai su wani asibiti mai zaman kansa domin a zubar da cikin, sannan ya damfare ta Naira miliyan biyu da sunan zai warkar da ita daga matsalolin boye da ke damun ta.
Duba da haka ne ta kai kara a caji ofis da ke Lafenwa a Abeokuta, lamarin da ya sa baturen ’yan sandan yankin CSP Muraina Ayilara ya jagoranci zuwa cocin amma suka iske wurin wayam.
Kakakin ’yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa daga baya Kwamishinan ’yan sandan jihar ya ba wa DPO din Lafenwa umarnin kamo fasto wanda suka gano shi a wurin da ya boye.
“A ranar Alhamis 6 ga watan Agustan 2020 muka kamo shi da misalin karfe 5 na yamma, ya kuma amsa tuhumar da ake masa.
“Ya ce ya ji labarin ’yan sanda na neman sa shi yasa ya gudu ya shiga buya”, inji shi.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Ogun, Edward Ajogun ya ba da umarnin binciken lamarin, ya kuma gargadi masu ci da addini su daina, su kuma al’umma su farga da irin wadannan bata-gari.