✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Daga yanzu a kira ni da Uwargidan shugaban kasa- Aisha Buhari

Aisha Buhari ta ce, daga yanzu a daina kiranta da suna ‘Wife of the President’ wato matar Buhari ta ce, yanzu ta zama uwargidan shugaban…

Aisha Buhari ta ce, daga yanzu a daina kiranta da suna ‘Wife of the President’ wato matar Buhari ta ce, yanzu ta zama uwargidan shugaban kasa ‘First Lady’.

Aisha Buhari ta yi, wannan kira ne a taron liyafar cin abinci da matan gwamnonin Najeriya suka shirya a gidan gwamnati da ke Abuja. Ta ce dama can ita tasa Buhari ya soke ofishin ‘Fist Lady’ Uwargidan shugaban kasa din.

Mai taimakawa Aisha Buhari a harkar watsa labarai Bisi Olumide-Ajayi, ta sanar da hakan.

Aisha, ta ce ta yi hakan ne kuma domin ceto matan Gwamnoni da suma ke samun matsala a jihohin su wajen kiran su da matsayin su.