Dan takarar Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya samu damar kai ziyara Amurka ne a makonni biyu da suka gabata sakamakon daga masa kafa na dan lokaci da hukumomin Amurka suka yi daga hukuncin hana shi shiga kasar da suka yi a shekarun baya kan badakar kudi. Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ne ya ruwaito haka, bayan ya tuntubi mutanen da suke da masaniya kan batun.
Tun farko, hukumomin Amurka ba su ce komai ba dangane da ziyarar Atiku zuwa kasar ba, kuma ba su ce komai ba dangane da haramcin da suka kakaba masa na hana shi shiga Amurka a shekarun baya ba. Amma wasu jakadun Amurka da sauransu da suke da masaniyar ziyarar tasa sun shaida wa Reuters cewa an haramta wa tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya shiga Amurka na tsawon shekaru masu yawa da suka shude, bayan da aka samu hannunsa a cikin wasu batutuwa biyu da suka shafi almundahana.
Magoya bayan Atiku sun bayyana cewa yadda gwaninsu ya shiga Amurka a ranar 17 da 18 ga Janairun da ya gabata ba tare da an kama shi ba, manuniya ce da ke tabbatar da cewa zargin da ake yi masa bai da tushe balle makama.
“Da ma labarin karya ne kuma mun tabbatar da haka,” inji Harold Molokwu, jami’in da ke jagorancin Jam’iyyar PDP a Amurka.
Jami’an Gwamnatin Amurka da dama sun ce Hukumar Al’amuran Cikin Gida ta Amurka ta daga wa Atiku kafa ne na dan lokaci, shi ya sanya ya samu damar kai ziyara kasar ba tare da an dauki matakin doka a kansa ba. Hakan kuwa ya tabbata ne bayan da mutanen Atiku suka yi ta kamun kafa a wurin hukumomin Amurka kan su kyale shi ya ziyarci kasar, domin yana daya daga cikin manyan ’yan takarar shugabancin Najeriya, babbar kasa a Afirka, a zaben da za a gudanar a makon gobe, don haka bai kamata su wulakanta shi ba.
Wani daga cikin mutanen da suke da masaniya kan batun, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce an kyale Atiku ya shiga Amurka ce saboda hukumomin kasar sun lura cewa yana da wata mamora gare su, idan har ya yi nasarar zama Shugaban Najeriya, babbar kasar da ta fi kowace girma a Nahiyar Afrika kuma wacce take kan gaba wajen samar da mai a nahiyar.
Mutanen da Atiku ya dauka haya, su ne suka roki hukumomin Amurka har suka amince masa ya shiga kasar ba tare da matsala ba, bayan ya biya Dala dubu 80, yayin da PDP kuma ta biya Dala dubu 90 kan haka. Sun gamsar da wasu daga cikin ’yan majalisar Amurka, musamman Mataimakin Sakataren Amurka mai kula da Al’amuran Afirka, Tibor Nagy cewa ya kamata Amurka ta taimaka wa dimokuradiyya a kasar bakaken fata mafi girma a duniya.
“Mataimakin Sakatare Nagy ya yi farin cikin ganawa da shi, inda suka tattauna al’amuran da suka shafi Amurka dangane da Najeriya, cewa suna bukatar a gudanar da zabe amsasshe kuma na gaskiya kuma cikin lumana da kwanciyar hankali da zai nuna gamsuwar al’ummar Najeriya,” inji wani jami’in Amurka.
Atiku dai ya fara gamuwa da matsalar shiga kasar Amurka ce tun lokacin da yake kan mulki a 1999 zuwa 2007. Sunansa ya fito karara a wata badakalar kudi da ta hada da wani tsohon Sanatan Amurka, William Jefferson, wanda aka zarga da cewa ya yi kokarin ba Atiku cin hanci domin fadada harkar kasuwanci a Najeriya. A shekarar 2009 dai an yanke wa Sanata Jefferson hukuncin daurin shekara 13 a gidan maza, duk da cewa daga bisani an sassauta masa yawan shekarun.
An samu rahotanni daban-daban, inda Atiku ya rika musanta zargin cewa ya aikata wani abu ba daidai ba. Ya ce babu inda shi ko matarsa suka taba fuskantar wani hukuncin aikata laifi a Amurka.