✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DAGA LARABA: Yadda ’Yan IPOB Suka Kashe Mai Tsohon Ciki Da ’Ya’yanta

Halin da ’yan Arewa ke ciki bayan IPOB ta kashe Malama Harida da ’ya’yanta kanana da wasu ’yan Arewa a Anambara

More Podcasts

Domin sauke shirin latsa nan

A wane hali ’yan Arewa mazauna Kudu maso Gabashin Najeriya suke ciki bayan ’yan kungiyar IPOB sun yi wa wata matar aure ’yar Arewa mai tsohon ciki tare da ’ya’yanta hudu kanana kisan gilla a Jihar Anambra?

Rahotanni da muka samu sun nuna kasa da awa 24 bayan kashe Malama Harira da ’ya’yan nata, ’yan haramtacciyar kungiyar sun kashe wasu ’yan acaba hudu, suka kone gawar daya daga cikinsu, sannan suka kashe wani mahauci, dukkansu ’yan Arewa.

Ku biyo mu domin jin abin da ya sa aka yi wa mai juna biyun, wato Malama Harira da ’ya’yanta kanana kisan gilla, da kuma irin halin da ’yan Arewa mazauna yankin Kudu maso Gabas suke ciki a halin yanzu.